Neja: Adadin Mutanen da Suka Rasu Ya Karu, Mutum Kusan 100 Sun Mutu
- Ana ci gaba da jimami da alhinin rashin da aka samu sakamakon iftila'in fashewar tankar mai da aka samu a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya
- Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin ya kai mutum 98
- Shugaban hukumar NSEMA, Aƙhaji Abdullahi Baba-Arah, ya bayyana mutane 69 sun samu raunuka yayin da shagunan ƴan kasuwa suka ƙone ƙurmus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankai mai ya ƙaru a jihar Neja.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a gobarar wacce ta auku a Dikko ya kai mutum 98.

Asali: Twitter
Shugaban hukumar NSEMA, Alhaji Abdullahi Baba-Arah, ya bayyana sabon alƙaluman mutanen da suka rasun ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Minna, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Abdullahi Baba-Arah ya ƙara da cewa, mutane 69 sun samu raunuka daban-daban a hatsarin, yayin da shaguna 20 suka ƙone ƙurmus, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Fashewar tankar mai ta jawo asarar rayuka a Neja
Hatsarin dai ya auku ne da safiyar ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:00, a kan titin Dikko-Maje, kusa da tashar mai ta Baddegi, a ƙaramar hukumar Gurara.
Lamarin ya faru ne lokacin da wata tanka da ke ɗauke da man fetur ta yi hatsari, sannan aka yi ƙoƙarin mayar da man da ta ɗauko zuwa cikin wata tanka daban.
A ƙoƙarin yin hakan, sai man fetur ɗin ya haɗu da janareton da ake amfani da shi wajen aikin, wanda hakan ya haifar da tashin gobarar da ta yi sanadiyyar rasa rayuka, raunata mutane da dama da asarar dukiya mai tarin yawa.
Gobarar ta jawo ƴan Najeriya da dama sun nuna alhini tare da aika saƙonnin ta'aziyya kan asarar rayukan da aka samu.
Gwamnatin tarayya da gwamnatin Neja sun yi ta'aziyya
Gwamnatin tarayya da ta jihar Neja sun yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da yin alƙawarin bayar da tallafi ga mutanen da suka jikkata da kuma waɗanda suka yi asarar dukiyoyinsu.
Gwamnatin Jihar Neja ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta kammala aikin hanyar Minna-Suleja, wacce aka ɗorawa alhakin jawo yawan haɗurra a yankin.
An binne gawarwaki a jihar Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa an birne gawarwakin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon iftila'in fashewar tankar mai a jihar Neja da ke yankin Arewa ts Tsakiya.
An gudanar da jana'izar mutanen da suka rasu waɗanda yawansu ya kai mutum 86 bayan aukuwar lamarin na ranar Asabar, 18 ga watan Janairun 2025.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja ta bayyana cewa an binne mafi yawa daga cikin mamatan a ƙabari ɗaya, yayin da aka tafi da wasu mutum biyar zuwa garuruwansu domin yi musu sutura.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng