An Ga Amfanin Bude Iyakokin Najeriya: Farashin Abinci Ya Karye a Wata Jihar Arewa
- Kasuwannin hatsi na fuskantar karuwar shigo da kaya daga kasashen makwabta wanda ya shafi 'yan kasuwa da manoma a Neja
- Farashin hatsi ya fadi sosai a Neja saboda kamfanoni na siyan kaya daga Chadi da Ghana, wanda ya kawo cikas ga manoman gida
- 'Yan kasuwa da manoma sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan da za su bunkasa hada hadar kayan hatsi na gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - An samu raguwar farashin kayan abinci a kasuwannin hatsi na jihar Neja sakamakon shigo da kaya daga kasashen Chadi, Ghana, Jamhuriyar Benin da Burkina Faso.
Wannan shigo da kayan abincin ya haifar da yawan hatsi a kasuwannin wanda ya yi tasiri sosai ga 'yan kasuwa, masu sayarwa da manoma.

Asali: Getty Images
Farashin hatsi ya sauka a jihar Neja
Masu adana hatsi suna fuskantar barazana ta asarar kudi mai yawa saboda kasuwannin da suka cika da buhunan hatsi amma ba a saye, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manoman kayan abinci da masu sayarwa sun shaida wa ‘yan jarida cewa yawan hatsi da ake shigo da shi ya dagula kasuwar, tare da rage ribar da ake samu.
Tazarar farashin hatsi na daga cikin dalilan da ke sa kamfanoni musamman masu samar da abincin dabbobi suka koma sayen hatsi daga kasashen makwabta.
'Yan kasuwar Neja sun koka da saukar farashi
Samun amfanin gona mai kyau a wadannan kasashe sun ba wa manoman su damar samar da hatsi mai yawa a farashi mai rahusa a Najeriya
Wani mai sayar da hatsi a Minna ya nuna damuwa, yana cewa:
"Mun yi tsammanin karin farashi, mun sayi hatsi mai yawa domin samun riba, amma shigo da kaya daga kasashen waje ya canza komai."
Masu adana hatsi da ke sa ran samun riba daga shigowar rani yanzu suna jin tsoro saboda wannan sauyi na kasuwa da ya shammace su.
Mutane na jin dadin saukar farashin hatsi
Wasu masu sharhi sun shaida wa manema labarai cewa idan wannan yanayin ya ci gaba, masu adana hatsi za su iya tafka asara mai yawa.
A gefe guda, masu saye suna farin ciki da saukar farashin, suna cewa wannan zai taimaka wajen rage dawainiyar rayuwa.
Duk da haka, manoman gida na ganin cewa raguwar farashin yana kawo barazana ga rayuwarsu.
"Kamfanoni sun fi son hatsin waje" - Hassan
Hassan Ango Abdullahi, shugaban kungiyar manoman hatsi da samar da shi ta Amana a karamar hukumar Shiroro, ya ce wannan yanayi zai shafi manoman cikin gid.
Mallam Hassan ya ce:
"Kamfanoni sun fi son siyan hatsi daga kasashen Chadi, Ghana da sauran kasashen saboda farashinsu ya fi sauki.
"A bara, kamfanoni suna gaggawar siyan masara daga garemu, amma wannan shekarar sun daina saboda farashin kasashen makwabta ya fi sauki."
Abdullahi ya roki gwamnati ta taimaka wa manoma ta hanyar samar da kayan aikin noma masu rahusa kamar taki, sinadarai da motoci.
Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin kasa
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin bude iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Wannan umarnin zai shafi dukkan iyakokin tudu da na sama, tare da cire takunkumai da aka sanya wa kasar a kwanakin baya.
Asali: Legit.ng