Bayan Birne Shi a Sokoto, an Cafke Wanda Ake Zargin Ya Harbe Jami'in EFCC a Anambra

Bayan Birne Shi a Sokoto, an Cafke Wanda Ake Zargin Ya Harbe Jami'in EFCC a Anambra

  • Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta ce ta na rike da wanda ake zargin ya bindige jami'inta a jihar Anambra
  • Matashin da ake zargi da damfara ta yanar gizo ya bindige jami'in EFCC a yayin kama shi kuma yana tsare a Enugu
  • An binne jami’in da ya rasu a Sokoto ranar Asabar, yayin da aka ceto wani jami’i da aka ji masa rauni yayin farmakin
  • Yan sanda sun ce sun kama wanda ake zargin tare da karbar bindiga daga wurinsa, kuma an fara bincike kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Enugu - Wani mutum da ake zargi da damfara ta yanar gizo ya kashe jami’in hukumar EFCC yayin wani samame a Anambra.

Wani jami’i na hukumar ya bayyana cewa wanda ake zargin ya bude wuta kan jami’an EFCC ranar Juma’a 17 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

An tsare wanda ake zargin ya bindige jami'in EFCC
Hukumar EFCC ta tabbatar da tsare wani da ake zargin ya harbe jami'inta a Anambra. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Twitter

Yadda jami'in EFCC ya rasa ransa a Anambra

TheCable ta ruwaito cewa yayin farmakin matashin ya kashe daya daga cikin jami'an kuma ya ji wa wani rauni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan wani jami’in hukumar EFCC ya rasa ransa sa'ilin da wasu ƴan damfara ta yanar gizo, Yahoo Boys, suka bude musu wuta a jihar Anambra.

Haka nan kuma wani jami’i a tawagar dakarun EFCC ya samu mummunan rauni kuma yana cikin mawuyacin hali a asibiti da ba a bayyana ba.

Kisan jami'in ya jawo maganganu a kafofin sadarwa yayin da wasu ke nuna jin dadi kan abin da ya faru, a bangare guda kuma wasu na jajanta wa.

An tsare wanda ake zargin kashe jami'in EFCC

An binne jami’in da aka kashe a Sokoto ranar Asabar 18 ga watan Janairun 2025 kuma yanzu wanda ake zargin yana tsare a ofishin EFCC da ke Enugu.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, bai maida martani kan tambayoyin da aka tura masa ba, duk da cewa an tabbatar da labarin kama wanda ake zargin.

Kakakin 'yan sanda a jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya kai farmaki kan jami’an EFCC, ya kashe daya, ya raunata wani.

Ikenga ya ce 'yan sanda sun kai dauki kan kiran gaggawa ranar Juma’a, sun kama wanda ake zargin, kuma sun kwace bindiga a wurin.

Ya kara da cewa an fara bincike kan lamarin, kuma za a sanar da karin bayanai nan ba da jimawa ba, cewar Punch.

EFCC ta tsare wasu daga cikin jami'anta

Kun ji cewa Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta tsare wasu daga cikin jami'anta.

Hukumar EFCC ta tsare jami'an ne guda 10 da ke aiki a ofishinta na Lagos bayan an nemi wasu kayayyakin aikin hukumar da ke hannunsu an rasa.

Shugaban hukumar EFCC ne ya ba da umarnin cafkewa tare da tsare jami'an har sai an kammala gudanar da bincike kan zargin da ake yi musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel