Wani Hamshakin Attajirin Najeriya Ya Bace, Matarsa Ta Jefi Gwamnati da Kalaman Zargi
- Matar Benjamin Ezemma ta nuna damuwa kan yadda jami'an tsaro da gwamnati ke gudanar da bincike kan bacewar mijinta
- Misis Ezemma ta zargi gwamnatin Anambra da nuna halin ko in kula game da sace mijinta, wanda ya kasance mai zuba jari a jihar
- Ta nemi hukumomin tsaro su bayyana wanda ake tuhuma da dauke mijinta da kuma yadda ake gudanar da bincike kan lamarin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Matar Benjamin Ezemma, attajiri kuma mai haɓaka gidaje a Anambra, Tochukwu Ezemma, ta roƙi jami'an tsaro su gano mijinta da ya bace.
Ezemma, wanda aka fi sani da BigBen, shi ne shugaban rukunin gidajen Dubai Estate da ke Awka, kuma an dauke shi a ranar 12 ga Nuwambar 2024.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa, Misis Ezemma ta yi zargin cewa gwamnatin Anambra tana nuna halin ko in kula game da batar mijinta, inji rahoton Vangaurd.

Kara karanta wannan
Jigawa: Gwamna zai ciyar da mabukata 189, 000 a Ramadan, an ji kudin da zai kashe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar attajirin ta koka kan bacewar Ezemma
Misis Ezemma ta shaida cewa mijinta ya kasance babban mai zuba jari a jihar, don haka bai kamata a dauki lamarin bacewarsa da wasa ba.
Sanarwar ta rahoto Misis Ezemma tana cewa:
"Ba zan iya zama shiru ba, fiye da watanni biyu ina wahala da ni da 'ya'yana da sauran iyalina. Ba zan ci gaba da yin shiru ba gaskiya.
"Ina kara tambayarsu, ina mijina kuma mahaifin 'ya'yana uku? Me ya faru da shi ne? Me yasa ba za a tattauna wannan matsalar ba?
"Sun shaida mana cewa dauke mijina yana da alaƙa da wani kasuwancin da suka gudanar amma aka samu akasi. Mijina ba wani ba ne a jihar Anambra."
Matar ta roki DSS ta nemo mata mijinta
Misis Ezemma ta ci gaba da cewa:
"Mijina ya yi karfi sosai ta hanyar yin ƙwazo a harkokin kasuwancinsa, kuma ya cancanci gudunmawar gwamnatin jihar a wannan lokaci.
"Ndi Anambra, don Allah ku taimaka ku tambaya mun hukumomi ko dokar binciken satar mutane ta canza ne, domin mijina ya bace, ba a gan shi ba har yanzu.
"Don Allah jama'a ku taimaka mun. Ina buƙatar sanin abin da ya faru da mahaifin 'ya'yana.
"Ina buƙatar amsoshi game da bacewar mijina. Waɗanne manyan mutane ne ya yi kasuwancin da su waɗanda ba za a gaya wa duniya ko a kama su ba?
"DSS ta ce lamarin yana kotu, cewa iyalinsa su nemi lauya don bin diddigin lamarin a kotu, amma muna buƙatar sanin wanda yake tuhumarsa? A kan me ake tuhumarsa?"
'Yan bindiga sun sace attajirin Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga a kan babura sun kai hari garin Kore, Dambatta da ke jihar Kano inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Bayan harin, sun sace wani attajirin ɗan kasuwa yayin da mazauna garin suka ce karamin yaro ya raunata bayan an harbe shi a kunnensa.
Asali: Legit.ng
