'Yan bindiga sun kai farmaki Kano, sun yi luguden wuta tare da sace attajiri

'Yan bindiga sun kai farmaki Kano, sun yi luguden wuta tare da sace attajiri

- 'Yan bindiga a kan babura sun shiga garin Kore dake karamar hukumar Dambatta ta jihar Kano

- Bayan luguden ruwan wutar da suka yi a daren Alhamis, sun tasa keyar attajirin dan kasuwa

- Duk da ba a samu rashin rai ko daya ba, mazauna garin sun ce karamin yaro ya raunata bayan an bindige kunnensa

Miyagun 'yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai farmaki jihar Kano kuma sun tasa keyar wani attajirin dan kasuwa dake karamar hukumar Dambatta a jihar.

'Yan bindigan sun kai farmakin garin Kore a tsakar daren Alhamis inda suka dinga ruwan wuta babu sassauci, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan mummunan hari yana zuwa ne bayan kwana daya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yayi korafin cewa miyagu sun fara tattaruwa a dajin Falgore dake jihar Kano.

KU KARANTA: Bishop Kuka yayi kira ga shugabannin Najeriya da su daina daukar rantsuwar da basu kiyayewa

'Yan bindiga sun kai farmaki Kano, sun yi luguden wuta tare da sace attajiri
'Yan bindiga sun kai farmaki Kano, sun yi luguden wuta tare da sace attajiri. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan miyagun makamai da aka samu bayan sojoji sun sheke dillalan makamai 3 a Sokoto

Legit.ng ta ruwaito yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci hukumomi da su yi hanzarin tarwatsa miyagun dake tattaruwa a dajikan Kano kafin al'amuransu su yi karfi.

Kamar yadda mazauna garin suka sanar, hantarsu ta kada sosai ganin masu harin sun shiga cikin gari a babura suna ruwan wuta, al'amarin da yasa mazauna yankin fadawa dajika cikin dare.

Sun sanar da cewa basu samu daukin jami'an tsaro ba koda aka kai farmakin, hakan yasa suka tasa keyar wani attajirin dan kasuwa a garin.

Mazauna garin sun sanar da cewa ba a yi asarar rai ko daya ba, sai dai wani karamin yaro ya samu rauni sakamakon harbin bindiga a kunne.

Muhammad Abdullahi Kore, shugaban karamar hukumar Dambatta ta jihar Kano ya tabbatar da satar attajirin dan kasuwar.

A wani labari na daban, hedkwatar tsaron Najeriya ta ce rade-radin da ake na cewa akwai yuwuwar ritayar wasu sojoji masu mukamin janar-janar bayan nadin da shugaban kasa yayi wa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban sojin kasa, ba gaskiya bane.

Mukaddashin daraktan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Abuja a ranar Alhamis, Daily Nigerian ta ruwaito.

Onyeuku yace murabus din wasu manyan hafsoshin sojoji a rundunar na sa kai ne, kari da cewa har yanzu rundunar bata aminta da ritayar wani hafsan soja ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel