Gwamna Ya Kafa Sabuwar Rundunar Tsaro a Jiharsa, Zai ba Masu Kwarmato Kyautar N5m
- Gwamnan jihar Anambra, Soludo, ya kaddamar da rundunar tsaro ta "Udo Ga-Achi" a ranar Asabar, 18 ga watan Janairun 2025
- Gwamna Chukwuma Soludo ya ce an hada jami'ai 2,000 a cikin Ugo Ga-Achi kuma za su samu taimako daga ‘yan sanda da sojoji
- Soludo ya sanya hannu kan Dokar Tsaron Anambra ta 2025, inda ya ayyana kyautar Naira miliyan biyar da masu kwartamo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, ya kaddamar da rundunar tsaro mai suna “Udo Ga-Achi” domin magance matsalar tsaro a jihar.
An rahoto cewa Gwamna Soludo ya kaddamar da rundunar “Udo Ga-Achi” a Awka, babban birnin jihar, a ranar Asabar, 18 ga Janairun 2025.

Asali: Twitter
Soludo ya kaddamar da rundunar tsaro
A yayin kaddamar da rundunar, Soludo ya ce zai rika bayar da kyautar Naira miliyan biyar ga masu bayar da bayanan sirri kan ayyukan 'yan ta'adda, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi rashi, an yi ta'aziyyar doki mai muƙamin 'Sergeant' a Kaduna, an yaba hadimarsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya sha alwashin cewa duk wanda ya taimakawa jami'an tsaro da bayanan mabuyar 'yan fashi, masu garkuwa da mutane ko mabuyarsu zai samu kyautar kudin.
Soludo ya ce:
"Muna kan daukar matakan gaggawa a kan tsaro tare da kaddamar da rundunar 'Udo Ga-Achi' domin yakar aikata laifuka da tabbatar da tsaro a Anambra.
"Muna bukatar al’umma su bayar da bayanai ga hukumomin tsaro ta hanyar kiran layin waya na kyauta a kan lamba 5111."
Anambra: Gwamna ya sanya kyautar kudi
Gwamna Chukwuma Soludo ya ci gaba da cewa:
"Ga masu bayar da bayanai, duk wanda ya ba da bayanai masu inganci da za su kai ga kama wani mai garkuwa da mutane ko dan fashi ko bayanai da za su kai ga tarwatsawar masu laifi za a biya shi kudi har zuwa Naira miliyan biyar (gwargwadon irin laifin)."
"Muna karfafa kowane gari da su tsara da aiwatar da shirinsu na tsaro. A kowane wata, za mu rika biyan garuruwan da ba a samu ayyukan laifi ba kyautar Naira miliyan 10."
Anambra: An fadi wadanda ke cikin tawagar tsaro
Soludo ya ce wannan tawaga ta hada da jami’ai 2,000 daga hukumomin tsaro daban-daban, ciki har da ‘yan sanda, sojojin Najeriya, sojojin ruwa, DSS da NSCDC.
Kungiyoyin fararen hula na tsaro, wanda aka fi sani da "Agunechemba," suna cikin tawagar.
Soludo ya ce gwamnati ta sayi motoci 200 na sintiri, kuma za a rarraba su a duk fadin jihar domin karfafa kokarin tsaron.
"Wannan rundunar za ta taimaka wajen yakar karuwar matsalar tsaro a Anambra, ciki har da garkuwa da mutane, fashi da makami, hada-hadar miyagun kwayoyi, da sauransu."
- A cewar gwamnan.
Gwamnan Zamfara ya kaddamar da rundunar tsaro
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya fara wani shiri na yaƙar ƴan bindiga da ke addabar jihar.
Ya ƙaddamar da sabon shahararren shiri na ‘Community Protection Guards,’ wanda zai tunkari ƴan bindigan kai tsaye.
Rundunar, wacce aka fi sani da Askarawan Zamfara, ta ƙunshi jami’ai 2,645, wadanda aka zaɓo daga ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Asali: Legit.ng