Sauƙi Ya Fara Bayyana, An Fara Sayen Shinkafa, Wake da Masara a Farashi Mai Araha
- Farashin abinci kamar shinkafa, wake, doya, garri, da taliya sun fara raguwa a kasuwannin Kaduna idan aka kwatanta da tsadar 2024
- Buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 wanda a baya ake siyar da shi N125,000 zuwa N130,000, yanzu ya ruguzo zuwa N120,000-N123,000
- ‘Yan kasuwa sun fara fitar da kayayyakinsu saboda tsoron asara, ganin cewa farashin kayan abinci ya fara sauka a farkon shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Mai yiwuwa an shiga 2025 da kafar dama yayin da rahotanni suka nuna an fara samun sauƙin tsadar kayan abinci a jihar Kaduna.
Bayanai sun nuna cewa kwanaki 17 da shigowar sabuwar shekara, kayan abinci sun fara araha fiye da yadda aka baro 2024 a jihar.

Source: Getty Images
Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya gudanar ya nuna cewa farashin kayan abinci kamar hatsi da sauran kayan masarufi sun fara raguwa a kasuwannin Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin kayan abinci ya fara araha
Rahoton ya tabbatar da cewa farashin kayan abinci kamar shinkafa, wake, doya, garri da taliyar yara sun sauka duk da ba wani rangwame sosai aka samu ba.
A kasuwar Sheikh Abubakar Gumi, wacce ita ce babbar kasuwar Kaduna, buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 da aka sayar N125,000 zuwa N130,000 a baya, yanzu ana sayar da shi tsakanin N120,000 zuwa N123,000.
Haka kuma, doya wacce farashin sa yake N7,00 a shekarar 2024, yanzu ta sauka zuwa tsakanin N5,000 zuwa N6,000, yayin da kananan doya suka sauka zuwa N2,500.
Yadda wake da shinkafa suka sauka
Kwanon wake mai cin kofi huɗi wanda a baya ake siyarwa tsakanin N3,000 zuwa N3,500, yanzu ya ƙara arha duk kwano ɗaya ya dawo N2,500, The Nation ta kawo.
Haka zalika, kwanon garri ya sauko zuwa N1,200 daga farashin da aka rika saye a kwanakim baya tsakanin N1,400 zuwa N1,500.
Wasu daga cikin kwastomomi masu sayen kayan abinci a kasuwar Kaduna sun shaidawa NAN cewa suna fatan wannan sauƙi da aka fara samu ya ɗore.
Hafsat Muhammad ta ce yanzu tana sayen lokar shinkafa a N2,100, sabanin farashinsa na baya N2,400, lokar masara da ake sayarwa N1,200 a baya, yanzu ta dawo N900.
Ƴan kasuwa sun fara fito da kayansu
Hajiya Ummi Shuaibu, wata ‘yar kasuwa, ta ce ta sayi buhunan masara bayan girbi da niyyar sake siyarwa bayan wasu watanni, amma ta canza ra'ayi tun da farashin kayan abinci ya fara sauka.
“Na yi tsammanin farashin zai tashi kamar na bara, amma hakan bai faru ba, don haka dole ne in fitar da kayan hannuna domin kar na yi asara.
“Buhun masara wanda a baya yake kan N60,000 yanzu yana tsakanin N50,000 zuwa N55,000, shi ya sa nake son sayarwa da wuri,” in ji ta.
Farashin shinkafa da wake ya sauka a Akure
Kun ji cewa farashin kayayyaki ya fara sauka a Akure, babban birnin jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
An ruwaito cewa farashin taliya, shinkafa da wake duk sun yi ƙasa amma kuma farashin manja da tattasai sun yi tashin gwauron zabi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


