Yadda Sojojin Najeriya ke Jefa Rayuwar Bayin Allah a cikin Matsala 'Bisa Kuskure'

Yadda Sojojin Najeriya ke Jefa Rayuwar Bayin Allah a cikin Matsala 'Bisa Kuskure'

Akalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin jirgin sama da aka a jihar Kaduna a 2023, an kai wani makamancin harin a Sakkwato a 2024 da wani a Zamfara a 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Hare-haren da sojojin saman Najeriya su ke kai wa a kan fararen hula bisa kuskure ya zama babbar matsala a yakin da dakarun su ke yi da ta'addanci a Arewacin kasar.

Soldiers
Kungiyoyi na fargabar yawan hare-haren sojoji a kan fararen hula Hoto: Amnesty International Nigeria/Nigerian Airforce HQ
Asali: Facebook

VOA ta ruwaito cewa sojoji sun farmaki jama'a ta sama a Zamfara a watan Janairu, 2025, inda mutane akalla 15 su ka koma ga Mahaliccinsu.

Legit ta tattauna da masu ruwa da tsaki, da su ka hada da jami'in gwamnatin Zamfara, Kungiyar Amnesty International a kan halin da jama'a a yankunan su ke ciki.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin sojoji: Wane taimako aka kai Zamfara?

Sulaiman Idris Bala, Mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal ya shaida wa Legit cewa gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakan gaggawa tun bayan harin garin Tungar Kara.

Ya ce:

"Hatsarin da ya faru ba fararen hula ya samu ba, jami'an tsaron bijilanti ne, sun zo kawo dauki sai abin ya same su.
An kai masu gudunmawa dai, wanda ba su da lafiya, an kai su asibiti, wanda su ka rasa mutane kuma an yi alkawarin taimaka masu.

Sulaiman Bala ya ce a matakin gaggawa, an samar da abinci da sauran kayan amfani da mutanen za su yi amfani da shi na tsawon lokaci, sannan tawagar sojoji ta ziyarci mutanen don ganin halin da su ke ciki.

Amnesty Int'l ta na fargabar hare-haren sojoji

A shafinta na Facebook, kungiyar da ke rajin fafutukar kare hakkin bil adama, Amnesty Int'i reshen Najeriya ya ce akwai bukatar a rika duba da kyau kafin kai farmaki a kan fararen hula.

Kara karanta wannan

Sojoji sun tsananta farautar Bello Turji, ana son kawo karshensa a kwanan nan

Shugaban kungiyar na Najeriya, Isa Sanusi ya shaida wa Legit cewa bai dace kokarin ceto 'yan kasa daga hare-haren.

A sanarwar da ta ce;

"Wasu daga cikin mazauna kauyen sun kone har lahira a cikin wutar da harin jirgin sama ya haifar. Dokar taimakon bil'adama ta kasa da kasa na bukatar a dauki duk matakan kariya da za a iya dauka don rage illar da za a iya kaiwa ga fararen hula."

Kungiyar na ganin irin wannan hare-hare ya na jefa rayuwar jama'a a cikin mawuyacin hali da rashin tabbas.

Harin sojoji a Kaduna ya takurawa jama'a

Jami'an tsaro sun yi kuskuren kai hare-hare a kan fararen hula a Kaduna, Sakkwato da Zamfara, inda rundunar ta jaddada cewa ta na bakin kokarinta domin kare afkuwar hakan a gaba.

A rahoton Daily Trust a 2024, mutanen Tudun Biri a Kaduna sun koka a kan yadda gwamnati ta ki cika alkawarin da ta dauka na taimakonsu tare da sake gina garin.

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

Gwamna ya jajanta harin sojoji a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya jajantarsa ga al'ummar jihar, musamman wadanda harin jirgin sama da sojoji suka shafa.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Zamfara za ta ci gaba da tallafawa dakarun sojoji da jama'ar garin a kokarinsu na tabbatar da tsaro a duk fadin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel