Daliba Ta Jagoranci Yunkurin Fille kan Malaminta a Kwalejin Kano

Daliba Ta Jagoranci Yunkurin Fille kan Malaminta a Kwalejin Kano

  • Wata daliba a Kwalejin Polytechnic ta Kano tare da saurayinta sun kai hari kan wani malami a Kwalejin fasahar
  • A cewar hukumar makarantar, saurayin dalibar ya yi yunkurin sare kan malamin a cikin ofishin da ke kwalejin
  • Jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin cafke dalibar da saurayinta a unguwar Dorayi, amma 'yan daba sun dakile yunkurin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Wata daliba a kwalejin fasaha a jihar Kano ta shirya kai hari kan wani malami mai suna Aliyu Hamza Abdullahi a ranar Talata, 14 Janairu, 2025.

Ana zargin dalibar, wacce kwalejin ba ta saki sunanta ba tare da saurayinta da kuma sun kutsa kwalejin tare da kai wa malamin hari a wani abu mai kama da son kashe shi.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a bikin nadin sarauta, ana fargabar an sumar da jami'ar NSCDC

Kano map
Daliba ta kai wa malaminta hari a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Leadership News ta ruwaito cewa malamin, wanda shi ne jami’in jarrabawa na sashen da dalibar ta ke karatu ya fada cikin barazanar iya rasa rayuwarsu a lokacin kai harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kai hari kan malami a Kano

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan dalibar ta nemi canja mata kwas din karatu zuwa wani sashe da ta fi so, saboda ba ta son sashen da ta ke.

Amma an shaida mata cewa makinta bai kai matakin da ake bukata don sauya mata kwas kamar yadda ta bukata ba, lamarin da ta ke ganin ba za ta amince da shi ba.

An tabbatar da kai wa malamin Kano hari

Jami’in hulɗa da jama’a na Kwalejin, Auwal Isma’il Bagwai, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Juma’a.

A cewar jami'in;

“Harin ya faru ne yayin da malamin ke cikin ofis dinsa yana kula da ɗalibai da misalin 2.00 n.r a ranar Talata. Dalibar ta shiga ofis din tare da saurayinta, tana nuna cewa malamin ne ya hana ta samun damar canjin sashen karatu.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi gargadin yiwuwar kai harin ta'addanci a Kano, an gano wasu bayanai

Sai saurayin ya fito da adda ya kai hari ga malamin, yana niyyar sare ma shi kai.”
“Malamin ya samu raunuka a hannuwansa yayin da yake kare kansa. Wasu daga cikin ɗaliban da ke ofis ɗin sun shiga tsakani, wanda hakan ya tilasta wa masu harin tserewa.”

Kano: Yadda aka kai malamin asibiti

Bayan kai harin, an garzaya da malamin zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci. Wata shaidar gani da ido, Aisha Goni, ta bayyana wa Legit cewa:

“Na zo wucewa daga wajen aiki a lokacin, na ga taron jama’a, sai na tsaya na ga an riko wani mutum jikinsa jini. A adaidaita sahu aka tafi da shi asibiti. Na ji ana cewa dalibar ta gudu.”

'Yan daba sun hana kama daliba a Kano

Jami’in kwalejin, Auwal Isma'il Bagwai ya ce jami’an tsaro na makarantar sun tafi unguwar Dorayi, inda dalibar da saurayinta ke zaune domin kama su, amma hakan ya ci tura.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun jefa mazauna Benuwai a tashin hankali, sun kashe mutane da dama

Ya kara da cewa;

“Da isarsu, dalibar ta shige gidansu, sannan wata tawagar ’yan daba suka fito dauke da makamai suka kai wa jami’an tsaron hari.”

Abba ya waiwayi daliban jihar Kano

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta sanar da fara rabon kayan makaranta kyauta ga dalibai sama da 789,000 a makarantun gwamnati 7,092 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa wannan shirin yana daga cikin kudirin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na inganta ilimi a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel