'Ɗangote Ya Buɗe Ƙofa, Farashin Litar Man Fetur Ya Sake Tashi a Najeriya

'Ɗangote Ya Buɗe Ƙofa, Farashin Litar Man Fetur Ya Sake Tashi a Najeriya

  • Farashin litar man fetur ya tashi zuwa tsakanin N1,050 da N1,150 bayan sanarwar matatar Ɗangote a ranar Juma'a
  • Wannan dai na zuwa ne bayan an yi hasashen tashin farashin fetur sakamakon hauhawar da ɗanyen mai ke yi a kasuwar duniya
  • Kungiyar ƴan kasuwa IPMAN ta ce a yanzu kowane lita za ta haura N1,000 a faɗin jihohin ƙasar nan saboda yanayin kasuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Farashin litar man fetur ya tashi zuwa tsakanin N1,050 zuwa N1,150 ya danganta da wurin da ka saya.

Wannan ƙari na zuwa ne bayan matatar Ɗangote ta ƙara farashin yadda za ta sayarwa da ƴan kasuwa kowace litar fetur ranar Juma'a.

Man fetur.
Farashin man fetur ya tashi a wuraren lodin yan kasuwa bayan karin matatar Ɗangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kamar yadda Punch ta tattaro, dillalan mai sun jaddada cewa za a ci gaba da samun ƙari a farashin fetur saboda yadda ɗanyen mai ke kara hauhawa a kasuwa.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin man fetur zai cigaba da tashi

A kwanakin bayan an ji shugaban kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa, Festus Osifo, na ishara da tashin farashin fetur.

Osifo ya yi hasashen cewa nan ba da dadewa ba mai zai ƙara tsada sakamakon yadda ɗanyen mai ke ƙara tashi a kasuwar duniya.

“Farashin danyen man ya tashi zuwa dala 80 a kowace ganga a yau (Alhamis). Idan har ba Naira ta ƙara kima a ƙasuwar canji ba, farashin PMS watau fetur zai karu a makonni masu zuwa," in ji shi.

Matatar Ɗangote ta sanar da sababbin farashi

A jiya Juma'a, 17 ga watan Janairu, 2025 aka samu ƙarin farashin kowace lita a matatar man hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote.

Matatar wadda aka kashe Dala biliyan 20 wajen ginata ta ƙara farashi daga N899 zuwa N955 da N950 a wurin lodin ƴan kasuwa.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

Wannan ƙari na matatar Ɗangote ya taba wuraren da ake kasuwancin man fetur, musamman a ma'ajiyar mai da kasuwanni masu zaman kansu.

Bincike ya nuna cewa gidajen ajiya masu zaman kansu duk da cewa suna da tsofaffin kaya, sun kara kudin lodin kowace lita zuwa N970 a Legas da N1,000 a Calabar.

Ƴan kasuwa sun bi sahun matatar Ɗangote

A tashar lodi mai zaman kanta ta Sahara, farashin fetur ya ƙaru da N20 zuwa N970 kowace lita daga N950 da aka yi ciniki a ranar Alhamis.

Ƴan kasuwa karƙashin ƙungiyar dillalan mai masu zaman kansu watau IPMAN sun yi hasashen ƙara farashin fetur, inda suka kace zai iya kai wa N1,100 a Legas.

IPMAN ta bayyana cews kowace litar mai na iya kai wa N1,150 a babban birnin tarayya Abuja saboda yanayin kasuwa.

Sakataren yada labarai na IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce yanzu haka za a koma sayar da fetur a farashin ya haura N1,000 a kowace lita.

Gwamnati ba ta da hannu a tsadar fetur

Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a yanzu babu ruwanta da batun ƙayyade farashin man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Ministan albarkatun man fetur na Najeriya ya ce yanayin kasuwa ne ke yanke farashin da za a sayar da kowace lita a yanzu amma babu hannun gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262