'Yan Sanda Sun Gano Ma'aikatar da ake Hadawa 'Yan Ta'adda Makamai

'Yan Sanda Sun Gano Ma'aikatar da ake Hadawa 'Yan Ta'adda Makamai

  • 'Yan sanda sun kai samame Benue, Delta da Kebbi, inda suka kama masu kera makamai da wasu masu laifi
  • An gano wata ma’aikatar kera makamai a Kwande, Jihar Benue, tare da kama mutum biyu da ke da hannu a lamarin
  • A daya bangaren, an cafke masu hannu a kisan kai da kuma kungiyar asiri tare da kwato makamai daban-daban

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu nasara kan wasu miyagu ta hanyar kai farmaki kan ma’aikatar kera makamai a jihar Benue.

Haka zalika jami'an sun kama wasu da ake zargi da kisan kai da shiga kungiyoyin asiri a jihohin Delta da Kebbi.

Yan sanda
'Yan sanda sun kai farmaki kan 'yan ta'adda a jihohi. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kama miyagun ne a cikin wani sako da kakakin 'yan sandan Abuja, Adejobi Olumuyiwa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano gidan da ake hada makamai

A ranar 11 ga watan Janairu, 2025, ‘yan sanda sun kai samame wata ma’aikatar kera makamai da ke yankin Tse Akamabe, a karamar hukumar Kwande a jihar Benue.

A yayin samamen, an kama mutum biyu da ake zargi da kera makamai, wadanda aka bayyana sunayensu da Friday Aduduakambe da Iorwashima Iornyume da aka fi sani “AK”.

Bayan gudanar da bincike a wajen, ‘yan sanda sun gano makamai da kayan kera su, wadanda suka hada da bindigun gida tara, bindiga mai kama da AK47 da ba a kammala ba.

Haka zalika an gano tukunyar gas biyu, injunan goge karfe hudu, da sauran kayan aiki, wanda hakan ya janyo aka yaba wa hukumomin tsaron daga bangarori daban-daban.

'Yan sanda sun farmaki 'yan kungiyar asiri

A wani lamari daban, jami’an ‘yan sanda a jihar Delta sun samu nasarar cafke wani shugaban kungiyar asiri mai suna Prosper Akeni, dan shekaru 32.

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

Daily Post ta wallafa cewa jami’an tsaro sun kai farmaki gidan Prosper Akeni ne bayan samun bayanan sirri.

An gano bindigogi daban-daban a hannunsa, ciki har da bindiga kirar revolver da Beretta, bindigun gida guda shida da harsasai 25.

An ruwaito cewa Prosper ya amsa cewa makaman sun kasance na kungiyar su ne, kuma shi ne ke kula da su.

An kama wanda ya yi kisa a Kebbi

A ranar 31 ga watan Disamba, 2024, an yi mummunan kisan kai a kauyen Bakin Turu, karamar hukumar Shanga, Jihar Kebbi.

An bayyana cewa wani matashi mai suna Yunusa Haruna, dan shekaru 25 ne ya caccaki dan uwansa, Isiyaku Haruna, da wuka a kirji har ya mutu.

A ranar 8 ga watan Janairu, ‘yan sanda sun kama wani mutum mai suna Abubakar Ummar a garin Zuru, bayan ya kashe wani mutum mai suna Mohammed Bala a wata hayaniya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Jawabin sufeton ‘yan sandan Najeriya

Sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya yaba wa jami’an tsaro kan wannan gagarumar nasara.

Ya kuma bukaci jama’a da su rika bayar da bayanai masu amfani ga ‘yan sanda domin ci gaba da inganta tsaro a Najeriya.

An yi hargowa kan kasafin kudin 'yan sanda

A wani rahoton, kun ji cewa an samu hargitsi a zauren majalisa yayin da sufeton 'yan sanda ke gabatar da bayani kan kasafin 2025.

Legit ta rahoto cewa rigima ta kaure ne yayin da wani Sanata ya ce sufeton 'yan sanda na karanto wasu bayanai da ba su cikin takardun da aka raba musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng