Gwamnatin Tinubu Ta Tara Gwamnoni da Manyan Jami'ai kan Kudirin Haraji

Gwamnatin Tinubu Ta Tara Gwamnoni da Manyan Jami'ai kan Kudirin Haraji

  • Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya halarci taron kwanaki biyu kan kudirin gyaran haraji da aka shirya a Abuja
  • Taron ya samu halartar gwamnoni daga jihohi daban-daban, ministoci, shugabannin hukumar FIRS, da sauran manyan jami’an gwamnati
  • Kwamitin shugaban kasa kan kudirin gyaran haraji, karkashin jagorancin Taiwo Oyedele ne zai yi wata tattaunawa da jami'an kan kudirin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya halarci taron kwanaki biyu na tattaunawa da gwamnoni kan kudirin haraji.

Taron, wanda ke gudana a dakin taro na Transcorp Hilton Hotel na karkashin jagorancin kwamitin shugaban kasa kan haraji tare da hadin gwiwar kungiyar gwamnoni.

Taron kudirin haraji
Gwamnonin jihohi sun hadu a Abuja kan kudirin haraji. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda taron ke gudana ne a cikin wani sako da kakakin gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Abba ya kwato motocin da jami'an gwamnatin Ganduje suka tsere da su a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin taron Abuja kan kudirin haraji

Taron ya mayar da hankali kan tattaunawa tsakanin gwamnonin jihohi da kwamitin shugaban kasa kan yadda kudirin haraji zai inganta tattalin arzikin kasa da jihohi.

Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele ne ke jagorantar tattaunawa kan kudirin haraji da ke gaban majalisar dokokin kasar nan a halin yanzu.

An bayyana cewa ana bukatar sake fasalin dokokin haraji domin tabbatar da cewa jihohi suna samun damar yin amfani da albarkatun kasa yadda ya kamata wajen samar da ayyukan cigaba.

Manyan da gwamnatin Tinubu ta tara

Taron ya samu halartar gwamnoni daga jihohi daban-daban na Najeriya, ciki har da shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara.

Hakazalika, ministoci masu ruwa da tsaki, shugaban hukumar FIRS, shugabannin ma’aikatu na jihohi ciki har da kwamishinonin kudi.

Haka zalika an tattaro kwamishinonin shari'a na jihohi da shugabannin hukumomin karbar haraji domin halartar taron a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamna ya duba halin da ake ciki, ya yiwa sarakuna karin albashi zuwa N350,000

Muhimmancin gyaran dokokin haraji

Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele, ya jaddada cewa gyaran dokokin haraji zai saukaka tsarin biyan haraji, tare da tabbatar da cewa jihohi suna cin gajiyar albarkatun kasa.

A cewarsa, yin haka zai taimaka wajen rage radadin talauci, samar da karin ayyuka, da kuma bunkasa rayuwar al’ummar Najeriya gaba daya.

Kwamitin ya yi alkawarin cewa duk wata shawara daga jihohi za ta kasance a cikin kudirorin gyaran dokokin da shugaba Tinubu ya mika ga majalisa.

Me ake tsammani bayan taron?

Ana hasashen cewa gwamnatin tarayya za ta shawo kan gwamnoni, musamman daga Arewa domin su amince da kudirin haraji bayan taron.

Sai dai duka da haka, za a jira kammala taron na tsawon kwanaki biyu domin ganin martanin da gwamnonin za su yi.

Taron na daga cikin matakan da aka dauka domin fahimtar da 'yan kasa tsarin haraji da kuma tabbatar da cewa kowa ya amfana daga tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi kunnen uwar shegu, duk da korafe korafe, za a tabbatar da kudirin haraji

Fasto ya soki tsare tsaren Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen fasto a Najeriya, Johnson Suleman ya soki tsare tsaren shugaba Bola Tinubu inda ya ce sun jefa kasa a wahala.

Duk da sukar da ya yi, Faston ya ce 'yan Najeriya ne suka jawo wa kansu shiga matsalar tattali sakamakon zaben tumun dare da suka yi a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng