Gwamna a Arewa Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Jiharsa, Zai Ɗauki Malamai 2,000 Aiki
- Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da ɗaukar malamai 2,000 aiki domin inganta bangaren ilimi a shekarar 2025
- Dauda Lawal ya bayyana cewa za a fara ɗaukar malamai 500 a tashin farko, tare da fadin sharudan tantance wadanda za a dauka
- Hakazalika, gwamnan ya fadi shirin gwamnatinsa na ginawa da kuma gyara sama da makarantu 400 a cikin shekarar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da ɗaukar malamai 2,000 aiki a fadin jihar, a cikin wani sabon mataki na gyaran ilimi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron Majalisar Zartarwa da ya jagoranta a dakin taro na gwamnatin jihar a Gusau.
Gwamnan Zamfara zai cika alkawari kan ilimi
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Channels TV ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa ɗaukar malamai na daga cikin alkawuran da Gwamna Dauda ya yi a lokacin yakin neman zabensa.
Sanarwar ta ƙara da cewa ilimi, wanda shi ne abu na biyu a cikin manufofin gwamnatin Dauda Lawal, ya samu kulawa sosai tare da samun nasarar da ake bukata.
Gwamna Dauda ya ayyana dokar ta baci kan ilimi
Sanarwar Sulaiman Bala ta ce:
"Gwamnan Dauda Lawal, a cikin kwazonsa na gyara ilimi a jihar Zamfara, ya ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi a jihar a ranar 14 ga Nuwamba, 2023.
"Dokar ta bacin da gwamnatin Zamfara karkashin gwamna Lawal ta ayyana ta haɗa da ginawa da gyara makarantu fiye da 400 a kananan hukumomin jihar 14.
"An samar da tebur mai zaman mutum biyu ga ɗalibai sama da 12,000 a makarantun kananan hukumomin 14 na jihar, kuma an kawo tebur 700 da kujeru 1,000 ga malamai."
Gwamnan Zamfara zai dauki malamai 2,000 aiki
A yayin da yake magana a taron, Gwamna Dauda ya bayyana cewa ɗaukar malamai aiki zai zama wani ɓangare na ayyukan gwamnatinsa a shekarar 2025.
"Gwamnatin za ta ɗauki malamai 2,000 da suka cancanta domin ingantawa da kuma farfado da bangaren ilimi a jihar.
"Za a ɗauki malamai a matakai don tabbatar da cewa an dauki mutanen da suka cancanta, musamman a darussan da ake da bukatar malamansu a makarantunmu.
"Wannan shirin na ɗaukar malamai yana cikin tsarin AGILE kuma zai magance lalacewar da aka samu a bangaren ilimi tare da inganta koyarwa."
- A cewar Gwamna Dauda Lawal, cikin sanarwar da Sulaiman ya fitar.
Yadda tsarin daukar aikin zai kasance
A cikin sanarwar, Gwamna Dauda ya ci gaba da cewa:
"Za mu fara daukar malamai 500 a cikin zangon farko na wannan shekara. A wannan lokaci, za a mayar da hankali kan daukar malamai a muhimman fannoni kamar Turanci."
"A cikin wannan tsarin, malamai za su mayar da hankali kan darussan da suka shafi lissafi, kimiyya, Pyshics, kimiyyar kwayoyin halitta, ICT da kuma nazarin kasuwanci."
Gwamnan na Zamfara ya tabbatar da cewa wannan shirin zai taimaka wajen inganta ilimi a jihar da kuma bayar da damar samun malamai masu kwarewa a fannoni masu muhimmanci.
Gwamna Dauda ya kwace lasisin makarantu
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamna Dauda Lawal ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimi a Zamfara don ceto jihar daga durkushewa.
Haka kuma, ya kwace lasisin makarantu masu zaman kansu yayin da ya koka kan lalacewar bangaren ilimi da ake fuskanta a jihar Zamfara
Asali: Legit.ng