Kwamishina ya bukaci N1bn domin gyaran makarantu 23 a Zamfara
Kwamishinan ilimi a jihar Zamfara, Ibrahim Abdullahi, ya ce gwamnati tana bukatar fiye da biliyan daya domin gyaran wasu makarantun sakandire guda 23 da ke jihar.
Ibrahim ya bayyana hakan ne ranar Talata a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, yayin da ya ziyarci wasu makarantun sakandire domin ganin halin da suke ciki.
A cewarsa, ya ziyarci makarantun ne don ganin irin kayan aikin da suke da su domin sanin yadda za a ingantasu, su dace da tsarin koyo da koyarwa.
"Na samu sahalewar mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, domin na gudanar da rangadin makarantun sakandire tare da sanar da shi hanyoyin da za a bi domin inganta yanayin makarantun.
"Gwamna ya damu matuka da tabarbarewar yanayin makarantu, kuma a shirye ya ke domin kawo gyara a bangaren harkar ilimi.
"Hakan ya hada da inganta nagarta malamai, daukan sabbi tare da horar da tsofin malamai da kuma inganta walwala da jin dadin malaman makaranta, musamman bayar da alawus ga malaman da aka tura aiki a yankunan kauyuka da karkara," a cewar kwamishina Ibrahim.
Kwamishinan ya bayyana cewa yawancin makarantun jihar suna bukatar gyara sakamakon wulakantar dasu da aka yi na tsawon shekaru, lamarin da ya ce ya kawo raguwar nagartar ilimi da aikin koyarwa a jihar Zamfara.
"Yanzu zamu mayar da hankali wajen inganta ginin makarantu, rage yawan malaman da aka dauka aro, daukan matasa masu kwazo da suke da nagarta ta zama malaman makaranta.
DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya bayar da umarnin cire shingen kan hanya da aka saka a iyakar Kano da Kaduna
"A yayin da muke yin wadannan aiyuka, ba zamu bari son rai da son zuciya su shiga gaban niyyar gwamnatinmu na kawo gyare - gyare masu amfani a bangaren ilimi ba.
"Za mu tabbatar da cewa mun dauki ma'aikata da suka dace, za mu samar da tsarin sani da kayyade adadin malaman makaranta da dalibai a dukkan makarantun sakandire 197 da ke fadin jihar Zamfara," a cewar kwamishinan.
A karshe, kwamishinan ya bukaci jama'a su cigaba da zage dantse wajen taimakawa gwamnatin gwamna Bello Matawalle da addu'a domin ta samu nasara a dukkan aiyukan da ta saka a gabanta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng