Tsofaffin Sojoji Sun Fallasa Masu ba Boko Haram Makamai da Kudi

Tsofaffin Sojoji Sun Fallasa Masu ba Boko Haram Makamai da Kudi

  • Tsofaffin manyan hafsoshin soja sun zargi wasu kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da taimaka wa Boko Haram da 'yan bindiga wajen samun taimako
  • Tsofaffin sojojin sun bayyana yadda rashin ci gaba, talauci, da jahilci ke zama dalilin da ke karawa kungiyoyin ta’addanci karfi a Najeriya
  • Sun yi kira ga gwamnati da ta kori kungiyoyin, da kuma neman taimakon Majalisar Dinkin Duniya wajen hana isowar makamai ga 'yan ta'adda

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsofaffin manyan hafsoshin soja sun bayyana damuwarsu game da yadda Boko Haram da 'yan bindiga ke ci gaba da yin tasiri duk da kokarin da sojoji ke yi na yaki da su.

A cewarsu, wasu kungiyoyi masu zaman kansu da wasu kasashen ketare suna taka rawa wajen tallafa wa 'yan ta'adda da kudi da makamai.

Kara karanta wannan

Tawagar sojoji ta sauka a Zamfara bayan harin da ya kashe bayin Allah

Sojoji
An zargi kungiyoyin sa-kai da tallafawa 'yan ta'adda. Hoto: HQ Nigerian Army|Nigeria Air Force HQ
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tsofaffin sojojin sun yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan kawo karshen lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ke rura wutar ta'addanci a Najeriya?

Wani tsohon kwamandan soji ya bayyana cewa matsalolin zamantakewa kamar rashin aikin yi, karancin ilimi da kiwon lafiya na kara ba Boko Haram damar daukar matasa.

Ya ce, a yankin Arewa maso Gabas da maso Yamma, akwai dimbin matasa da ba su da aikin yi ko wata hanyar dogaro da kai.

A cewarsa,

“Yawancin matasa a Borno, misali, suna fitowa fili su ce suna shirin tafiya yankin Tumbuns domin shiga Boko Haram saboda ba su da wani abin yi.”

Bugu da kari, tsohon kwamandan ya bayyana cewa wasu manoma suna bai wa 'yan ta’adda kayan amfanin gona a matsayin haraji wanda ke taimaka musu wajen cigaba da ayyukansu.

Su waye masu taimakon Boko Haram?

Kara karanta wannan

Tinubu ya jaddada shirin ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya

Tsohon daraktan yada labaran sojojin Najeriya ya ce yana da tabbacin cewa wasu kungiyoyin kasashen waje na taimaka wa Boko Haram wajen samun kudi da makamai.

Tsohon daraktan ya ce;

“'Yan ta'adda suna samun kudi daga ketare ta hanyar hada-hadar kudi ba bisa ka’ida ba, da kuma wasu kasashe masu daukar nauyin ta’addanci a yankin Sahel.”

Ya kuma yaba wa kokarin Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) wajen kama wadanda ke daukar nauyin Boko Haram, amma ya koka cewa babu matakin hukunci da aka dauka a kan su.

Bukatar taimakon majalisar dinkin duniya

Hafsoshin sun goyi bayan Janar Christopher Musa na neman Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka wajen gano hanyoyin da makamai da kudi ke zuwa hannun 'yan ta’adda.

Sun ce yin hakan zai taimaka wajen toshe duk wata kafa da ke kawo makamai da kudi ga Boko Haram da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa ya faɗawa gwamnatin Tinubu dabarar murƙushe ƴan ta'adda cikin sauƙi

Korar kungiyoyin kasashen waje daga Arewa

Wani tsohon kwamandan rundunar sojojin sama ya bayyana cewa wajibi ne gwamnati ta kori duk kungiyoyin kasashen waje da ke aiki a Arewacin Najeriya cikin sa'o'i 72.

Ya yi zargin cewa kungiyoyin ne ke boye gaskiya da kuma ba da tallafin kudi da makamai ga ‘yan ta’adda.

Tsohon sojan ya kara da cewa, matakin korar kungiyoyin zai taimaka wajen rage tasirin su a cikin rikicin Najeriya.

An kashe masu neman raba Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun soji sun ragargaji wasu 'yan ta'adda da dama masu fafutukar raba Najeriya biyu.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun samu nasarar ne a wani samame da suka kai tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sandan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng