Gwamnatin Tarayya Ta Yi Raddi ga Sanusi II kan Sukar Tsare Tsaren Tinubu
- Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan kalaman Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, dangane da sauye-sauyen tattalin arziki na gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Bayanai sun nuna cewa ta ce ba ta bukatar amincewar Sanusi II domin aiwatar da manufofinta, duk da cewa tana maraba da ra’ayin duk wani ɗan Najeriya
- Gwamnatin Tinubu ta jaddada muhimmancin hadin kai, tare da kira ga Sanusi II da sauran shugabanni su fifita muradin kasa a kan bukatun kashin kansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta bukatar amincewar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, domin tabbatar da sauye-sauyen tattalin arziki.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin da yake mayar da martani ga kalaman Sanusi II kan manufofin tattalin arzikin gwamnati.
Mohammed Idris ya bayyana haka ne a cikin wani sako da ma'aikatar Yada Labarai ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin ta bayyana cewa manufofin da take aiwatarwa suna da nufin tabbatar da ci gaba mai dorewa da farfado da tattalin arzikin Najeriya, ba tare da la’akari da son zuciya ba.
Martanin Tinubu kan kalaman Sanusi II
Ministan Yada Labarai ya ce kowa yana da damar fadin albarkacin baki, amma ya nuna rashin jin dadi kan yadda Sanusi II ya ce ba zai goyi bayan sauye-sauyen ba saboda dalilai na kashin kansa.
Mohammed Idris ya ce;
“Najeriya tana cikin wani yanayi da ake ake bukatar daukar kwararan matakai domin shawo kan matsalolin tattalin arziki.
"An aiwatar da sauye-sauyen gwamnati ne ba da wata manufa ba sai saboda suna da muhimmanci ga ci gaban kasa.”
Muhimmancin sauye-sauyen gwamnati
Gwamnati ta jaddada cewa matakan da ta dauka, kamar cire tallafin man fetur da daidaita darajar Naira, sun kawo gagarumar nasara ga tattalin arziki.
The Cable ta wallafa cewa ministan ya jaddada cewa daidaita darajar Naira ya kara bunkasa kudin ajiyar kasar wajen Najeriya.
“Wannan gwamnatin na aiki tukuru domin tabbatar da ci gaba mai dorewa, wanda zai amfanar da al’ummar Najeriya gaba daya,”
- Ministan yada labarai
Kira ga Sanusi II da sauran shugabanni
Gwamnati ta bayyana takaicin yadda Sanusi II, wanda ke da kwarewa a fannin tattalin arziki, ya koma sukar manufofin da ya taba goyon baya a baya saboda wasu dalilai na kashin kansa.
Ta yi kira gare shi da sauran shugabanni su zama masu kishin kasa tare da fifita muradin Najeriya a kan ra’ayoyin kashin kansu.
“Lokaci ya yi da za mu hada kai mu yi aiki tare don tabbatar da cewa Najeriya ta cimma burinta na zama kasa mai ci gaba da walwala,”
- Mohammed Idris
Manufar gwamnatin Tinubu ga kasa
Gwamnatin shugaba Tinubu ta jaddada cewa burinta shi ne jagorantar Najeriya zuwa ga bunkasar tattalin arziki.
Ta kuma yi alkawarin cewa za ta ci gaba da karbar shawarwarin masu kishin kasa, amma za ta kasance mai jajircewa wajen fifita muradin al’ummar Najeriya.
Kokarin Tinubu kan tsaron Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa zai cigaba da kokari wajen magance matsalolin tsaro.
Bola Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin bikin tunawa da 'yan mazan jiya, ya ce zai cigaba da kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng