Gwamna Ya Daina Boye Boye, Ya Gano Manufar Sojojin da Suka Kashe Bayin Allah a Zamfara

Gwamna Ya Daina Boye Boye, Ya Gano Manufar Sojojin da Suka Kashe Bayin Allah a Zamfara

  • Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa harin sama da ya kashe mutane sama da 16 a kauyen Tungar Kara ba da gangan sojoji suka yi ba
  • Dauda Lawal ya ce sojojin sun saɓa saiti ne a lokacin da suke yaƙar ƴan bindigar da suka kai hari yankin, amma ba haka kurum suka farmaki jama'a ba
  • Gwamnan ya gamsu sojoji za su kawo karshen ta'addancin ƴan bindiga a Zamfara, inda ya ce saura kiris Bello Turji ya baƙunci lahira

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce ba da gangan sojojin sama suka farmaki fararen hula da ƴan banga ba kwanan nan.

Gwamna Lawal ya bayyana cewa shi da kansa ya nemi rundunar sojoji ta kawo masa ɗauki domin kakkaɓe ƴan bindigar da suka addabi yankin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Lokutan da sojoji suka kai hare hare kan mutane bisa kuskure daga 2024 zuwa yau

Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.
Gwamnan Zamfara ya ce ba da gangan sojoji suka farmaki jama'a ba a kauyen Tungar Kara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Dauda Lawal ya bayyana haka ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin sama sun yi ksukuren kashe mutum 16

Daily Trust ta ruwaito cewa, an kashe mutane 16 da suka hada da ’yan banga da fararen hula a wani harin da sojojin sama suka kai a Tungar Kara da ke karamar hukumar Maradun.

Da farko rundunar sojin sama ta musanta kuskuren amma daga bisani ta ce za ta gudanar da bincike don gano haƙiƙanin abin da ya faru.

Gwamna Dauda ya faɗi abin da ya faru

Da yake jawabi kan asalin abin da ya faru, Gwamna Dauda Lawal ya ce shi ya kira sojojin sama su kawo ɗauki kauyen bayan ƴan bindiga sun farmaki al'umma.

Gwamnan ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, inda ya ce ba da gangan sojojin suka kashe fararen hula ba, kuskure ne.

"Ina da cikakken bayanin abin da ya faru a wannan rana, saboda mu muka kira sojoji bayan samun labarin ƴan bindiga sun kai hari kuma suka amsa suka kawo ɗauki, sun kashe ƴan ta'adda da yawa.

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa ya faɗawa gwamnatin Tinubu dabarar murƙushe ƴan ta'adda cikin sauƙi

"A karo na biyu da muka kira su, abin takaici kuma suka farmaki wasu daga cikin ƙauyukan da suke koƙrin ceto, garin haka ne suka kashe waɗanda ba ruwansu, ina da yaƙinin ba da gangan ba ne."
"Ba da gangan sojoji suka kashe fararen hula da ƴan banga ba, garin yaƙar ƴan bindiga ne hakan ta faru."

Dauda Lawal.

Rundunar sojin sama ta tura wakilai

Gwamnan ya ƙara da cewa hafsan sojojin saman Najeriya ya kafa kwamiti wanda ya zo jajantawa gwamnatin Zamfara da al'ummar da wannan kuskuren ya shafa.

Ya ce kwamitin ya ziyarci wurin domin duba ainihin abin da ya faru da nufin ɗaukar matakan kare faruwar haka nan gaba.

Dauda Lawal ya ce yana da ƙwarin guiwar cewa sojoji na da ƙarfin da za su murkushe ƴan bindiga gaba ɗaya a cikin abin da bai wuce wata guda ba.

Ya ce kwanakin Bello Turji a duniya sun kare domin nan ba da jimawa ba zai bakunci lahira kamar yadda sojoji suka sheƙe gawutattun ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Mutanen gari sun yi tara tara, sun kama babban mawaƙi ɗauke da kan mace

Tawagar sojojin sama ta isa Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa tawagar rundunar sojojin sama ta kai ziyara Zamfara domin duba abin da ya faru da kuma yi wa al'umma jaje kan kurkuren da suka yi.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin rundunar sojin ta yi na gudunar da bincike kan zargin hefa bama-bamai kan waɗanda ba ruwansu a Tungar Kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262