Sanatan Arewa Ya Faɗawa Gwamnatin Tinubu Dabarar Murƙushe Ƴan Ta'adda cikin Sauƙi

Sanatan Arewa Ya Faɗawa Gwamnatin Tinubu Dabarar Murƙushe Ƴan Ta'adda cikin Sauƙi

  • Sanata Ali Ndume ya ce Najeriya za su samu galaba a yaki da Boko Haram idan aka samar da karin jiragen yaki ga sojojin kasar nan
  • Dan majalisar dattawan ya jaddada bukatar gwamnati na maida hankali kan tsaro da jin dadin jama’a yayin gudanar da kasafin kudi
  • Game da alakarsa da shugaban kasa, Sanata Ndume ya ce yana girmama Bola Tinubu amma yana sukar manufofinsa don ya yi gyara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Ali Ndume, ya ce za a samu galaba sosai kan Boko Haram idan aka samar da karin jiragen yaki.

Maganar Sanata Ndume na zuwa ne yayin da Legit Hausa ta rahoto cewa mayakan Boko Haram sun kashe kimanin manoma da masunta 40 a Borno.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bugi karji kan darajar Afrika a Qatar, ya fadi sirrin cigaban nahiyar

Sanata Ali Ndume ya fadawa gwamnatin Tinubu sirrin kawo karshen 'yan ta'adda cikin sauki.
Sanata Ali Ndume ya bukaci gwamnatin Tinubu ta siyo karin jiragen yaki don murkushe Boko Haram. Hoto: Senator Ali Ndume
Asali: Facebook

Dan majalisar dattawan ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a shirin 'siyasa a yau' na gidan talabijin din Channels a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ya kawo dabarar murkushe 'yan ta'adda

Sanata Ali Ndume ya ce sojojin Najeriya za su iya murkushe 'yan ta'adda amma suna bukatar karin kudade don bunkasa ayyukansu.

Ya bayyana rashin kayan aiki da karancin kwarin gwiwa a matsayin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga yaki da ta’addanci.

A cewarsa, sojojin da ke fagen fama na samun N1,500 ne kawai a matsayin kudin alawus na yau da kullum.

"Ina girmama Tinubu" - Sanata Ali Ndume

Sanatan ya nuna damuwa kan halin da tattalin arziki ke ciki a karshin mulkin Tinubu, yana mai cewa masu ba shugaban kasa shawara ne ke jagorantar sa ba daidai ba.

Duk da haka, Ndume ya bayyana cewa yana girmama shugaban kasa Bola Tinubu yayin da ake kallonsa a matsayin mai sukar gwamnatinsa kai tsaye.

Kara karanta wannan

"Ku murkushe su": Zulum ya nemi agajin sojoji da ƴan bindiga suka kashe manoma 40

Sanata Ndume ya musanta zargin cewa yana nuna rashin ladabi ga Tinubu, inda ya ce shi ba ya sukar shugaban kasar, yana sukar wasu manufofinsa kawai.

“Ba na sukar shugaban kasa, amma ina sukar manufofinsa. Wannan gwamnati tamu ce, kuma ina yi ne domin a kawo gyara."

- Sanata Ali Ndume.

Ndume ya fadawa Tinubu inda zai gyara

Ya bayyana yadda Tinubu ya halarci bikin aurar da ’yarsa duk da cewa ya yi daidai da ranar tunawa da sojojin Najeriya da suka sadaukar da rayuwarsu ga kasa.

Sanata Ndume ya ce:

"Bayan taron, na yi tunanin zai tafi, amma ya ce ba zai tafi ba har sai an kammala bikin auren.”

Dangane da manyan matsalolin kasa, Ndume ya yi kira ga shugaban kasar da ya maida hankali kan aiwatar da kasafin kudi da ba da fifiko ga bangarori masu mahimmanci.

Sanata Ndume ya ce ya sha fadawa shugaban kasa cewa

Kara karanta wannan

Harin sojoji: Gwamna ya jajanta, ya yaba wa jami'an tsaro kan tarwatsa yan bindiga

"A aiwatar da kasafin kudi, ka maida hankali kan tsaro da jin dadin jama’a, sauran abubuwa za su gyaru.”

Ndume ya ziyarci sojoji bayan harin Boko Haram

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Ali Ndume ya ziyarci hedikwatar Operation Hadin Kai a jihar Borno, domin jajanta wa iyalan wadanda suka rasu.

Ya yi ta’aziyya ga iyalai da al’ummar Sabon Gari na karamar hukumar Damboa, inda Boko Haram suka kai harin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka.

Sanata Ndume ya yabawa sojoji saboda jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da yin addu’a ga wadanda suka ji rauni a harin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.