Abba Ya Yabi Jami'i Mai Amana, Kwamitin Rabon Kayan Makaranta Ya Maido Rarar N100m
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa kwamitin rabon kayan makaranta bisa gaskiya da rikon amanar gwamnati
- Gwamnan ya ƙaddamar da rabon kayan makaranta 798,000 ga ɗaliban Firamare, wanda za a ci gaba duk shekara
- Abba Kabir Yusuf ya roƙi tallafin jama’a da kamfanoni wajen farfaɗo da harkar ilimi domin amfanin yaran jihar Kano
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa kwamitin da ke kula da rabon kayan makaranta ga ɗaliban makarantun firamare a jihar. Yabon na zuwa ne bayan da kwamitin ya dawo da Naira miliyan 100 daga cikin Naira biliyan 2 da aka ware don aikin ga gwamnatin jiha bayan an samu rarar kudin.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamna ya nuna matuƙar farin ciki da rikon amana na kwamitin.
Yayin ƙaddamar da rabon kayan makaranta guda 798,000 ga ɗaliban Firamare a fadar gwamnatin Kano, Gwamna Yusuf ya ce irin wannan gaskiya na kwamitin alama ce ta rikon amanar gwamnatinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya yabi kwamitin rabon kayan makaranta
Hadimin gwamna kan kafafen sada zumunta, Salisu Yahaya Hotoro, ya wallafa a shafin Facebook cewa Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa kwamitin rabon kayan makaranta a jihar.
Ya ce kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Tajo Othman, ya nuna kishin jihar, gaskiya da rikon amana.
Gwamnan ya ce da sun so, za su iya yin almubazzaranci da kuɗaɗen da suka rage, amma saboda tsoron Allah, sun dawo da su domin tallafa wa wasu ayyukan raya jihar Kano.
Gwamnan Kano ya yaba da ingancin kayan dalibai
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba da ingancin kayan makarantar da aka samar, ya tabbatarwa da al’umma cewa wannan shiri zai zama na kowacce shekara don inganta ilimi a fadin Kano.
Haka kuma, ya bayyana cewa akwai shirin rarraba kwamfutoci ga makarantun sakandare a jihar domin ɗalibai su samu ƙwarewar amfani da fasahar zamani don samun damammaki a gaba.
Gwamna Abba ya nemi taimakon jama'a
Gwamnan ya yi kira ga masu hannu da shuni da ƙungiyoyin kasuwanci su tallafa wa gwamnatinsa wajen farfaɗo da harkar ilimi a jihar. Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, duk da irin cigaban da gwamnatin ke samu, gudunmuwar jama'a na iya yin tasiri wajen sauya rayuwar ɗalibai da ke faɗin Kano.
Gwamna Abba ya waiwayi daliban Kano
A baya kun ji cewa gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ƙaddamar da shirin rarraba kayan makaranta kyauta ga ɗalibai 789,000 a faɗin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa shirin ya haɗa makarantu 7,092 a ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda za a raba kayan ga yara maza da mata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng