Matawalle Ya Gano Abin da Ake Bukata don Magance Rashin Tsaro a cikin Watanni 2
- Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya koka kan ƙarancin kuɗin da ake warewa ma'aikatarsa a cikin kasafin kuɗin Najeriya
- Matawalle ya bayyana cewa da a ce akwai isassun kayan aiki, da za a iya kawo ƙarshen ƴan bindiga a jihar Katsina cikin watanni biyu
- Ƙaramin ministan ya buƙaci ƴan majalisa da su ƙarawa ma'aikatar tsaro kuɗaɗe a kasafin kuɗi domin a samu damar magance matsalar ƴan bindiga
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan hanyar kawar da ƴan bindiga a jihar Katsina.
Bello Matawalle ya bayyana cewa sojojin Najeriya za su iya kawar da yan ta’adda daga dazuzzukan Katsina cikin watanni biyu idan aka ba su motocin yaƙi guda 50.
Matawalle ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata yayin da ya bayyana gaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai domin kare kasafin kuɗin ma’aikatar tsaro na shekarar 2025, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin ƴan shekarun nan, yankin Arewa maso Yamma na Najeriya ciki har da jihar Katsina, sun sha fama da matsalar ƴan bindiga.
Ministan tsaro ya koka kan rashin kuɗi
Ministan ya ce Naira biliyan 50 da gwamnatin tarayya ta warewa ma’aikatar tsaro a kasafin kuɗin 2025, ya yi kaɗan wajen magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa kasafin kuɗin shekarar 2025 ya ragu da Naira biliyan 18 idan aka kwatanta da wanda aka warewa ma'aikatar a shekarar 2024.
Ya ce duk da rashin wadatattun kuɗaɗe, mutane na sa ran su yi abin al’ajabi wajen magance matsalar rashin tsaro.
Bello Matawalle ya buƙaci a samar da kayan aiki
Ƙaramin ministan ya ce mutane na ta ƙorafi cewa ana warewa ɓangaren tsaro maƙudan kuɗaɗe, amma abin da ake ware ba ya isa.
"Ku duba kasafin kuɗin 2025, an ware mana Naira biliyan 50 kawai. Na je Sokoto ba tare da wani ya ɗauki nauyina ba, na yi hakan ne domin na tabbatar da cewa mutane suna iya kwanciya su yi barci ba tare da fargaba ba."
“Abokin aikina Abubakar Badaru, wanda shi ne ministan tsaro, ya je Zamfara da Katsina, amma ba wani tanadi a kasafin kuɗin domin ya yi hakan."
“A zahiri, ma’aikatar tsaro ya kamata ta samar da wasu kayayyakin aiki ga wasu yankuna, amma ba za mu iya ba. A cikin kasafin kuɗin 2024, mun samu damar samar da motocin ƴaki masu sulke (APC) guda 20 kawai."
“Me motoci masu sulke guda 20 za su iya yi? A Katsina kaɗai, idan za mu iya samun APC guda 50 da za su shiga dazuzzuka su fatattaki ƴan ta’addan, ina tabbatar muku cewa cikin watanni biyu za mu kammala magance matsalar ƴan bindiga."
“Ina son ku fahimta, matsalar tsaro tana ko ina a ƙasar nan, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas. Amma ku duba kasafin kudin 2025, Naira biliyan 50 kacal aka warewa ma’aikatar tsaro."
- Bello Matawalle
Matawalle ya buƙaci ƴan majalisar da su yi la’akari kan yiwuwar ƙarawa ma’aikatar tsaro kuɗaɗe domin ta samu damar siyo kayan aiki don magance matsalar tsaro a Najeriya.
Jami'an tsaro sun yi galaba kan ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka wasu ƴan bindiga da ke addabar mutane a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng