Matasa Na Jiran Karin Albashi: NYSC Ta Aika Muhimmin Sako ga Masu Bautar Kasa
- Hukumar NYSC ta karyata wani labari da ke cewa masu jiran zuwa horo su je ofisoshinta na jihohi don karbar lambobin 'kira'
- NYSC ta ja hankalin matasan da su kara yin hakuri, su kuma ci gaba da bibiyar shafukanta domin ganin sababbin bayanai
- Hukumar kula da masu bautar kasar ta bayyana damuwa kan yada labarai marasa tushe da nufin haifar da rudani ga matasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar da ke kula da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta aika muhimmin sako ga matasa masu shirin yiwa kasa hidima a rukunin C zangon shekarar 2024.
Hukumar NYSC ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa matasa masu shirin yi wa kasa hidima da ba su karɓi lambobin gayyata ba, su tafi ofisoshinta na jihohi.
NYSC ta karya jita-jitar tura matasa jihohi
Bayanin hakan na kunshe a cikin sanarwar da Caroline Embu, daraktar bayanan jama'a ta wucin gadi ta rabawa manema labarai a ranar Talata, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce hankalin hukumar ya kai kan wata jita-jita da wasu bata gari ke yaɗawa cewa matasa masu shirin yi wa kasa hidima su tafi ofishin NYSC na jihohi.
Hukumar NYSC ta ce waɗannan saƙonnin ba daga gare ta suka fito ba, kuma ta roƙi jama'a musamman masu shirin yiwa kasa hidima da su yi watsi da su.
NYSC ta fadi hanyoyinta na isar da sako
Sanarwar Caraline Embu ta ce:
"Jama'a suyi watsi da wadannan saƙonnin domin ba su fito daga hukumar ba, kuma ba gaskiya bane."
NYSC ta tabbatar cewa duk wata hulɗa da matasa masu shirin yi wa kasa hidima ana yin ta ne ta shafinsu na yanar gizonta ko kuma shafukan hukumar na soshiyal midiya.
"Su ci gaba da duba shafukansu na yanar gizonmu, kuma su duba shafukan sada zumunta na NYSC (Facebook, X, Instagram, Threads) don ganin sababbin bayanai."
- A cewar sanarwar Caroline.
Hukumar ta ƙara da cewa matasa masu shirin yi wa kasa hidima da ba su karɓi lambobin gayyatarsu ba har zuwa yanzu su kara yin haƙuri.
Hukumar NYSC ta roki matasa su kara hakuri
Sakamakon wannan jinkiri da aka samu, NYSC ta roƙi matasan da su ci gaba da duba shafukanta akai-akai don samun sababbin bayanai daga hukumar.
Hukumar ta bayyana cewa ba a bayar da lambobin gayyata daga jihohi ba, kuma duk wani bayani yana kan dandalin NYSC.
"Jama'a suyi hankali da jita-jitar da ba daga hukumar suka fito ba, su bi doka da ka'ida a kowane lokaci,"
- inji sanarwar.
Matasa masu shirin yi wa kasa hidima a rukunin C karkashin zangon shekarar 2024 sun shiga damuwa na rashin samun lamba ko takardar gayyata daga hukumar NYSC.
An fadi lokacin kara alawus din NYSC
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban NYSC, Birgediya Janar Yusha'u Ahmed, ya kwantar da hankalin matasa masu yi wa ƙasa hidima game da alawus na N77,000.
Janar Yusha'u ya tabbatar da cewa matasan za su fara karɓar sabon alawus daga gwamnati nan ba da jimawa ba, kuma za a kare haƙƙoƙinnsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng