Minista Ya Jawowa Tinubu Abin Magana da Ya Ce Zai Kashe N8bn a Wayar da kan Jama'a
- Ma’aikatar wuta tana shirin kashe N8bn domin wayar da kan ‘yan Najeriya kan biyan kudin lantarki da kare kayayyakin wuta
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa an tsara wayar da kan al’umma don rage sata da inganta biyan kudin wuta
- Cif Adebayo Adelabu, wanda ya samu mukamin Minista a 2023, ya ce wannan shiri zai taimaka wajen gyara tarbiyyar al’umma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya ta shirya kashe Naira biliyan 8 don wayar da kan ‘yan Najeriya kan biyan kudin lantarki a kan lokaci a 2025.
Ministan wutar, Adebayo Adelabu, ya bayyana hakan ranar Litinin yayin da yake kare kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamitin majalisa na wuta.
"Dalilin kashe N8bn a wayar da kai"- Ministan wuta
Adelabu ya bayyana cewa akwai bukatar wayar da kan ‘yan Najeriya kan muhimmancin kare kayayyakin wutar lantarki a kasar, inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bayyana cewa, hana satar wutar lantarki wani bangare ne na dalilan wayar da kan al’umma da ma’aikatar ke son cimmawa.
Mista Adelabu ya ce:
“A fannin wayar da kai, muna ganin al’ummarmu na bukatar a tunatar da su cewa kayayyakin wuta mallakar kasa ne baki daya.”
"Akwai bukatar gyara tarbiyar al'umma" - Adelabu
Ministan ya kara da cewa:
“Ya kamata al’ummarmu su sani cewa akwai bukatar su guji satar wutar lantarki. Idan sun ga wani abu, ya kamata su sanar.”
“Akwai bukatar al’umma su san muhimmancin biyan kudin lantarki a kai-a kai. Duk wadannan abubuwa na bukatar isar da sako ta hanyar wayar da kai.”
"Mun yi imani cewa bangaren wutar lantarki na bukatar gudanar da manyan ayyukan wayar da kai da kuma gyaran tarbiyyar al’umma.”
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya himmatu wajen ganin an inganta sashen wutar lantarki a Najeriya tun bayan karbar ragamar jagorancin ma’aikatar.
Ya hau mukamin ministan wuta a ranar 21 ga Agusta, 2023, tare da kudurin sauya tsarin wutar lantarki na kasar nan.
Kafin wannan mukami, Adelabu ya taba kasancewa mataimakin gwamnan bankin Najeriya a bangaren sashen ayyuka, daga 2014 zuwa 2018.
Adelabu ya rike mukamai a gida da waje
Hakazalika, Adelabu ya yi takarar gwamnan jihar Oyo a jam’iyyar APC a 2019, duk da cewa bai yi nasara ba.
An san Adelabu da gogewarsa a bangaren kudi da banki, inda ya taba rike manyan mukamai a gida da waje.
Ma’aikatar wuta tana fatan wannan shirin wayar da kai zai inganta fahimtar al’umma kan muhimmancin biyan kudin lantarki da kare kayayyakin wuta.
'Yan Najeriya sun yi wa minista martani
Legit ta tattaro wasu daga martanonin da 'yan Najeriya suka yi a shafukansu na X.
@shehu_mahdi ya ce:
"Kawai don wayar da kan mutane, za a kashe N8bn. Abin mamaki ba ya karewa. 'Yan Najeriya 320,000 za su iya kwanan farin ciki idan aka raba masu N25k kowanne daga wannan N8bn din."
@waxdigitals ya ce:
"Wasu lokutan idan ina karanta biliyoyin nan, na kan yi mamaki matuka, kuma sai in tambayi kaina, wai dama muna da tarin kudi haka amma aka bar tituna da gine gine a lalace? Najeriya ta lalace."
@bulama_abbas ya ce:
Ban fahimci abin da ke faruwa da duk waɗannan hukumomi da ma'aikatun ba. Ba abin da suka iya sai sata kuma Tinubu ya ki korarsu."
@torty_mercy ta ce:
"Gwamnatin tarayya ta ba ni N10m. Zan tattaro bayan abokan huldar da ke shan wuta a Najeriya. Zan yi masu wannan bitar sannan zan tura sakonni ga wadanda aka tantance su.
"Allah ya hukunta APC."
@latitudeXtwit ya ce:
"Ya kamata su yi amfani da Naira biliyan 8 din wajen biyan kudin wutar lantarkin yan Najeriya."
Dan Najeriya ya sha wutar N47m a wata
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mohammed Jameel, wanda aka fi sani da White Nigerian, ya ce mutane na satar wutar lantarki fiye da kima a kasar nan.
White Nigerian ya ce akwai wani mutumi da ya sani da ke satar wutar lantarki da ta kai kimar Naira miliyan 14 duk wata yayin da shi yake biyan Naira miliyan 47.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng