Matashi Ya Doke Mahaifiyarsa da Sanda, Ya Kashe Ta, Ya Wurga Gawa a Rijiya
- ’Yan sanda sun kama Mathias Amunde bisa zargin kashe mahaifiyarsa da sanda a karamar hukumar Obudu, jihar Cross River.
- An ce wanda ake zargin tare da wani abokinsa sun yi amfani da sanda wajen kashe tsohuwar, sannan suka jefa gawarta cikin rijiya
- ’Yan sanda sun tabbatar da cewa za a ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma daukar matakin da ya dace a bisa doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Cross River - Wani matashi mai suna Mathias Amunde ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin kashe mahaifiyarsa ta hanyar amfani da sanda a Cross Rivers.
Bayan kisan, an ce Mathias da wani abokinsa mai suna Walcot sun jefa gawar mahaifiyar tasa a cikin rijiya, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.
Punch ta wallafa cewa 'yan sanda sun tabbatar da cewa za a ci gaba da bincike kan lamarin domin tabbatar da gaskiya da kuma hukunta wadanda suka yi aika-aikar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda matashi ya kashe mahaifiyarsa
Jaridar PM News ta wallafa cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin da ake yi masa tambayoyi a ofishin ’yan sanda.
Mathias ya bayyana cewa shi da abokinsa Walcot sun yi amfani da sanda wajen kashe mahaifiyar tasa.
Matashin ya ce;
“Ni da Walcot ne muka kashe ta. Mun yi amfani da sanda muka kashe ta.
Bayan mun kashe ta, Walcot ya ja gawarta zuwa bayan gida, sannan muka dauke ta tare muka jefa a cikin rijiya.”
Bayan haka, Walcot ya tsere daga wurin da lamarin ya faru, yayin da Mathias ya shiga hannun hukuma.
'Yan sanda sun tabbatar da kama Mathians
Kakakin rundunar ’yan sanda na jihar Cross River, Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ta yi da manema labarai a ranar Litinin.
Irene Ugbo ta ce;
“Eh, mun kama shi, kuma za mu mayar da shi hedikwatar rundunar domin ci gaba da bincike a ranar Talata.”
Irene ta kara da cewa lamarin ya saba wa dabi’u da al’adun mutunta iyaye, domin haka za a yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata laifin.
Halin da ka shiga bayan gano Mathians
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, inda jama’a suka yi tir da wannan mummunan aikin na kashe uwa, wacce ta zama ginshikin rayuwar mutum.
Jama'a sun bayyana takaicinsu da alhini kan abin da ya faru, suna masu cewa akwai bukatar a gurfanar da duk wadanda suka shiga cikin wannan danyen aiki a gaban shari’a.
Sun kuma yi kira ga hukumomi da su tabbatar da cewa an gudanar da bincike mai inganci domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Kiran 'ya sanda ga jama'a
’Yan sanda sun yi kira ga jama’a da su ba da hadin kai wajen bayar da bayanai masu amfani domin kammala bincike cikin sauri.
Ana ganin lamarin ya sake jaddada bukatar al’umma su kara kula da dabi’un tarbiyyar yara, tare da kokarin hana aikata miyagun laifuffuka.
Saurayi ya sare kan budurwarsa
A wani rahoton, kun ji cewa wani mai waken yabo ya kashe budurwarsa a tsakanin jihar Nasarawa da birnin tarayya Abuja.
An kama matashin yayin da yake kokarin guduwa a kusa da wani coci bayan ya sare kan budurwarsa ya sanya shi a cikin buhu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng