Saurayi ya kashe mahaifiyarsa saboda zaman dadiro da saurayi a gidansu

Saurayi ya kashe mahaifiyarsa saboda zaman dadiro da saurayi a gidansu

- Wani saurayi da ya hau dokin zuciya ya haike wa mahaifiyarsa tare da zama silar rasa ranta

- Saurayin, mai shekaru 21 a duniya, ya bukaci mahaifyarsa ta daina mu'amala da maza barkatai

- An samu rashin jituwa a tsakaninsu bayan mahaifiyar ta sanar da matashin cewa haka ta ke son rayuwarta

A ranar Asabar ne aka kama Wani matashin saurayi, ma'aikacin gona, mai shekaru 21 a Karnataka da ke yankin Haveri a ƙasar Indiya, bisa zargin aikata fyaɗe da kashe mahaifiyarsa.

Ƴansanda sun ce saurayin yana zargin mahaifiyarsa da mu'ammalar aure da mazaje iri daban daban. Shi kuma yace mata ta daina mu'ammalantar mazajen, amma sai taƙi.

Da yammacin 12 ga watan Nuwamba,2020, mahaifiyar da ɗanta suka kaure da musu, inda baya nan ne ya aikata taɓargaza ta hanyar yi mata fyaɗe da kasheta har lahira.

Acewar ƴansanda a Shiggion, mahaifiyar saurayin mai shekaru 40, wacce itama ma'aikaciyar gona ce, suna zaune tare da ɗanta a gidansu dake Vanahalli.

Saurayi ya kashe mahaifiyarsa saboda zaman dadiro da saurayi a gidansu
Saurayi ya kashe mahaifiyarsa saboda zaman dadiro da saurayi a gidansu @Thenation
Asali: Twitter

Mijin matar ya rasu shekaru sha biyar da suka gabata, kuma tana mu'amala da wani mutumi da suke unguwa ɗaya.

Mazauna yankin sun tseguntawa ɗanta cewar tana mu'amala da mazaje iri-iri.

Sanadiyyar wannan batu, matashin ya sha faɗa da mahaifiyarsa a lokuta da dama a can baya.

Ƴansanda sun ce sati guda kafin ya aikita kisan, saurayin mai shekaru 21 yayi musayar yawu da mahaifiyar tasa akan lallai sai ta rabu da saurayinta.

"Mahaifiyar ta gaya masa cewar ita tana son rayuwa da saurayinta saboda haka ba zata iya yanke alaƙa tsakaninta da shi ba. Hakan ya haddasa zazzafan musu a tsakaninsu," acewar ƴansandan Shiggion.

Da safiyar ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba, mahaifiyarsa da ƴar'uwarta sun je gona girbar shuka. Suka kammala, suka dawo gida.

Ƴansanda sun ce anan ne saurayin ya tilasta mata shan barasa. Daga nan kuma ya janyo ta zuwa gona kusa da titin Gangibhavi.

Nan suka fara jayayya, sai kawai saurayin ya hankaɗa mahaifiyarsa ƙasa, ya yi mata fyaɗe, sannan ya shaƙe mata wuya har ta mutu.

Da safiyar ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamba 2020, lokacin da ƴar'uwar mahaifiyar tasa ta biyo mata domin su tafi aikin gona, sai saurayin ya shaida mata cewa mahaifiyar tasa ta riga ta wuce gona tun kafin ta ƙaraso.

Da taga har dare ya yi 'yar uwarta ba ta dawo gida ba, sai ita da mijinta suka haɗa jama'a domin a fita neman ta. Anan ne suka tsinci gawarta a gonar dake kusa da titin Gangibhavi da misalin ƙarfe tara 9pm na dare.

Ƴar'uwar mamaciyar ta shigar ta ƙorafi gaban ƴansanda, inda ta bayyana musu cewar ana yawan samun cece-kuce tsakanin marigayiyar da ɗanta.

"Ni da ɗiyata mun fara zargin yana da nasaba da mutuwarta, saboda mun tsinci gawarta a yashe, kayanta kuma a tuɓe. Mun tambaye shi sau da dama ranar Juma'a, 13 Nuwamba, ko ya san inda ta shiga amma sai ya yi mana ƙarya.

Da ƴansanda suka tambayeni lokacin da na shigar da ƙorafin akan ko ina zargin wani da hannu a kisan, sai na faɗi sunansa.Ƴar'uwar marigayiyar ta shaidawa jaridar TNM, kamar yadda The Nation ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel