Abba Ya Waiwayi Daliban Kano, Ya Shirya Yin Abu 1 da Zai Ragewa Iyaye Kashe Kudi

Abba Ya Waiwayi Daliban Kano, Ya Shirya Yin Abu 1 da Zai Ragewa Iyaye Kashe Kudi

  • Gwamnatin Kano za ta raba kayan makaranta kyauta ga yara dalibai 789,000 a makarantu 7,092 don ƙarfafa karatun yara a jihar
  • Gwamna Abba Yusuf zai yi hakan ne domin rage yawan yaran da basa zuwa makaranta tare da tallafa wa iyayen da ba su da hali
  • Kwamishinan watsa labaran Kano, Ibrahim Waiya ya yi bayanin shirin da Gwamna Abba ya yi na bikin kaddamar da rabon kayan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin jihar Kano, karkashin Abba K. Yusuf ta ce za ta fara raba kayan makaranta kyauta ga dalibai 789,000 daga yau Litinin.

Wannan bayani ya fito ne a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Waiya, ya fitar ranar Lahadi.

Gwamnatin Kano ta yi magana kan rabawa dalibai kayan makaranta kyauta
Abba da kansa zai rabawa daliban Kano sama da 789,000 kayan makaranta kyauta. Hoto: @Kyusufabba, @GoranMagaji
Asali: Twitter

Gwamna Abba zai rabawa dalibai kayan makaranta

Ibrahim Waiya ya bayyana cewa wannan tsari yana daga cikin kudirin Gwamna Abba Yusuf na inganta ilimi a jihar, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa zai kashe N7bn a gyaran cibiyoyin kiwon lafiya 88 cikin watanni 4

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya ce sama da yara 789,000 maza da mata daga makarantu 7,092 a ƙananan hukumomi 44 na jihar za su ci gajiyar shirin.

"Manufar shirin ita ce ƙarfafa karatun yara da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar ba kowa damar samun ilimi mai nagarta."

- A cewar kwamishinan.

Dalibai 789,000 za su samu kyautar kayan makaranta

Ibrahim Waiya ya kara da cewa wannan tallafi zai taimaka wa iyayen da ba su da halin biyan kuɗin kayan makarantar yayansu.

“Sama da dalibai maza da mata 789,000 a makarantun gwamnati 7,092 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar ne za su karbi kayan a karkashin shirin."

- A cewar Ibrahim Waiya.

Ya ce hakan na nuna cewa ilimi shine babban ginshiki a kudurorin gwamnatin Abba Kabir Yusuf da nufin kawo ci gaba a ko’ina cikin jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa fifita bukatun dalibai zai taimaka wajen ba su damar samun ilimin da za su yi nasara a rayuwarsu idan sun girma.

Kara karanta wannan

Ya na ji ya na gani: Dalilai 5 da za su iya hana gwamnan APGA samun tazarce a 2025

Abba ya dage don inganta ilimi a Kano

Hakan nan kuma, Kwamred Ibrahim Waiya ya ce ba yara ingantaccen ilimi zai ba su damar bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma ta sana'o'i da ayyuka daban daban.

Ibrahim Waiya ya ce:

"Gwamnati na neman karfafawa yara manyan gobe da ilimi da kwarewar da suke bukata domin samun nasara da kuma ba da gudummawa mai kyau ga al'umma."

Kwamishinan ya bayyana cewa za a fara taron kaddamar da shirin da karfe 1:00 na rana a dakin taro na Coronation Hall da ke cikin Gidan Gwamnatin Kano.

Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ne da kansa zai jagoranci tsarin rabon kayan makarantar a wurin bikin.

Abba zai gina makarantu 3 kan N8bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware N8bn domin gina makarantun firamare a jihar Kano tare da samar da kayan aiki.

Kara karanta wannan

Abba ya dauko yaki da talauci gadan gadan, ya raba jarin Naira biliyan 2.1 a Kano

Makarantun za su tallafawa yara masu basira daga gidajen marasa karfi domin inganta iliminsu da kyautata makomarsu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a gina makarantun a kowace babbar mazaba, kuma N6bn za a kashe wajen gyaran wasu makarantun firamare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.