Gwamnatin Zamfara Ta Saɓa da Sojoji kan Kisan Fararen Hula Yayin Farmakin Ƴan Ta'adda
- Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Dauda Lawal ta tabbatar da kisan fararen hula a harin da sojojin sama suka kai kan ƴan ta'adda
- Tabbatar da kisan ya musanta iƙirarin da rundunar sojojin sama ta yi na cewa babu shaidar da ke nuna cewa fararen hula sun rasu sakamakon harin
- Gwamnatin wacce ta yabawa sojoji kan farmakar ƴan ta'addan ta ce za ta ba da tallafi ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon farmakin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta yi magana kan harin da rundunar sojojin sama ta kai kan ƴan bindiga da ake zargin ya yi sanadiyyar rasa ran fararen hula.
Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Dauda Lawal ta musanta iƙirarin da rundunar sojojin ta yi, kan cewa babu cikakkiyar shaida cewa fararen hula 16 sun mutu a harin da aka kai a Tungar Kara, ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi sojoji da kisan fararen hula a Zamfara
A ranar Juma’a, dakarun sojojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma, sun kai farmaki kan ƴan ta’adda a ƙaramar hukumar Maradun.
Bayan kai harin, rahotanni daga al’ummar yankin sun bayyana cewa fararen hula 16, ciki har da wasu mambobin rundunar Askarawan Zamfara da ƴan sa-kai sun rasu a yayin farmakin.
Rundunar sojojin sama ta musanta wannan zargi, tana mai cewa babu wata cikakkiyar shaida da ke tabbatar da rahotannin.
Me.gwamntin Zamfara ta ce kan harin sojoji?
Sai dai, a sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce wasu mambobin rundunar Askarawan Zamfara da ƴan sa-kai sun rasa rayukansu yayin harin.
Gwamnan bai bayyana adadin yawan fararen hular da suka mutu ba a sakamakon harin da aka kai kan ƴan ta'addan.
"Mun samu rahotanni masu kyau da dama dangane da hare-haren da rundunar sojojin sama ta Najeriya ta kai a ƙananan hukumomin Maradun da Zurmi a ƙarshen mako."
“Wannan farmakin ya raunana ƙarfin ƴan ta’adda sosai kuma ya nuna jajircewar rundunar sojojin sama wajen cika aikinta na kare fararen hula da tsare rayuka da dukiyoyin al’umma."
“Duk da wannan nasara, abin takaici ne cewa wasu mambobin rundunar Askawaran Zamfara da ƴan sa-kai sun rasa rayukansu yayin farmakin a Tungar Kara.”
- Gwamna Dauda Lawal
Gwamnan ya tabbatarwa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu cewa gwamnati za ta ba su dukkan goyon baya da tallafin da suke buƙata.
Sojoji sun kashe shugaban ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wani shugaban ƴan ta'adda a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma.
Sojojin sun yi nasarar hallaka Sani Rusu a wani harin da suka kai a yankin Bamamu na ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Jami'an tsaro sun daɗe suna farautar Sani Rusu wanda ya yi ƙaurin suna wajen addabar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Asali: Legit.ng