Gwamna a Arewa Zai Kashe N7bn a Gyaran Cibiyoyin Kiwon Lafiya 88 cikin Watanni 4
- Gwamnatin Kogi za ta kashe N7bn don gyara cibiyoyin lafiya 88 a kananan hukumomi 21 da goyon bayan Babban Bankin Duniya
- Gwamna Usman Ododo ya ce shirin gyara cibiyoyin zai tabbatar da kiwon lafiya mai inganci da isasshen kayan aiki ga al’umma
- Ododo ya bukaci al’umma da shugabanni da su rika sa ido kan cibiyoyin lafiyar, yayin da ya yaba wa kokarin tsohon gwamnan jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Gwamnatin Kogi za ta kashe sama da N7bn don gyara cibiyoyin lafiya 88 a kananan hukumomi 21 na jihar.
Ismaila Isah, mai bai wa gwamna Usman Ododo shawara kan harkokin yada labarai, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Kogi: Gwamna zai gyara cibiyoyin lafiya 88
Ododo ya bayyana hakan ne yayin bikin miƙa ayyukan gyaran ga 'yan kwangiloli a cibiyar lafiya ta MPHC da ke Felele, Lokoja inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan, wanda Abdulazeez Adams, kwamishinan lafiya na jihar ya wakilta, ya ce gyaran cibiyoyin ya dace da kudirin gwamnatinsa na inganta kiwon lafiya.
"A sabuwar shekarar 2025, mun kaddamar da shirin gyaran cibiyoyin lafiya 88, wanda zai ƙara daga darajarsu, kuma kari ne kan guda 70 da ake kan gyarawa."
- A cewar Usman Ododo.
Babban Bankin Duniya ya ba da gudunmawa
Gwamnan ya ci gaba da cewa:
"Wannan ci gaba ne mai nuni da aniyar mu ta samar da kiwon lafiya mai inganci da kuma tabbatar da cewa kowa yana da damar samun kiwon lafiya daga matakin farko."
"Tare da goyon bayan Babban Bankin Duniya, gwamnatin jihar Kogi ta ware sama da N7bn don wannan aiki na musamman."
Ododo ya mika godiya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan fifita kiwon lafiya a matakin ƙasa.
Gwamna ya bukaci kammala aiki a wata 4
Ya kuma yaba wa tsohuwar gwamnatin Yahaya Bello da ta gina harsashin ci gaban kiwon lafiya a jihar.
Ya yi kira ga 'yan kwangilar da su bi ka’idojin aikin kuma su kammala ayyukan cikin watanni huɗu kamar yadda aka tsara.
Ododo ya bukaci 'yan kwangilar da su yi aiki tare da shugabannin al’umma don tabbatar da aiwatar da ayyukan yadda ya kamata.
Ododo ya nemi hadin kan al'ummar Kogi
Hakanan, ya bukaci al’ummomi da su ɗauki nauyin kula da cibiyoyin lafiyar, kayan aiki, da kuma ma’aikata.
Gwamnan ya umarci hukumomin gwamnati, masu ruwa da tsaki, tare da jagorancin ma’aikatar lafiya ta jihar, da su sa ido kan ayyukan sosai.
Ya ce aikin gyaran cibiyoyin zai kawo sauyi a fannin kiwon lafiya, wanda zai inganta rayuwar al’ummar jihar baki ɗaya.
Ododo ya ziyarci Shugaba Tinubu a Villa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya gana da Gwamna Ahmed Usman Ododo a fadar shugaban ƙasa, Abuja, ranar Laraba, 15 ga watan Mayu.
Gwamna Ododo ya tattauna kan tsaro, musamman bayan hare-haren 'yan bindiga da ake yawan samu a jihar a 'yan kwanakin nan, ciki har da satar dalibai.
Asali: Legit.ng