Kasashe 10 na Afrika da ke da asibitoci da tsarin kiwon lafiya masu inganci
Cibiyar kiwon lafiya bangare ne mai matukar amfani a kowacce kasa wanda bai kamata a nuna masa halin ko-in-kula ba. Akwai wasu kasashen Afrika da ke da cibiyoyin lafiya masu matukar inganci.
Da gudumawar The African Exponent, Legit.g ta kawo muku kasashe 10 masu ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a Afrika a 2020.
An hadu a wannan ittifakin ne ta bayanai daga kungiyar kiwon lafiya ta duniya, ma'aikatun lafiya da kuma masu lura da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu.
1. South Africa
Kasar Afrika ta kudu ce kasa mai cibiyoyin kiwon lafiya mafi inganci. Akwai asibitoci masu zaman kansu a kalla 200 a kasar wadanda ke iya fito na fito da asibitocin Turai, Asia da Amurka.
2. Tunisia
Kasar Tunisia na da cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati wadanda ake kula da su ta harajin da Caisse Nationale d’Assurance Maladie ke samarwa. A hakan ake samar da magani ga yawancin kasar baki daya.
3. Kenya
A kasar Kenya, haihuwa da awo duk kyauta ne. Kasar ta kankare kudin asibiti ga kananan yara, mata masu ciki da kuma haihuwa.
Kasar tana bada tallafi tare da inshorar kiwon lafiya ga tsofaffi da kuma nakasassu.
KU KARANTA: Kurunkus: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana 'yan majalisar da suka karbe kwangilar NDDC
4. Algeria
A kasar Algeria, asibitocinsu duk na gwamnati ne kuma kowanne dan kasa na iya zuwa ya samu magani kyauta.
5. Nigeria
Akwai asibitocin kudi da na gwamnati. Sakamakon rashin kula da gwamnati bata bada wa da kuma rashin ma'aikata, asibitocin gwamnatin basu da inganci.
Amma a bangaren na kudi ko kuma masu zaman kansu suna da matukar inganci.
6. Egypt
7. Morocco
8. Rwanda
9. Tanzania
10. Zambia
A wani labari, ma'aikatan lafiya a Najeriya sun bayyana yadda suke rayuwa yayin barkewar cutar korona a cibiyar killacewa ta jihar Legas da kuma gwagwarmayar da suke yi.
Dakta Adeola Aderele ta ce ba abu bane mai sauki gwagwarmayar da take. Amma kuma ba za ta iya zama ta kalmashe kafa ba tare da yin komai ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng