Bello Turji na Tsaka Mai Wuya, Sojojin Najeriya Sun Yi wa Yaransa Ruwan Wuta a Zamfara

Bello Turji na Tsaka Mai Wuya, Sojojin Najeriya Sun Yi wa Yaransa Ruwan Wuta a Zamfara

  • Sojojin sama sun yi luguden wuta kan yaran kasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma
  • Mai magana da yawun rundunar, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewaya ya ce sun sheke ƴan bindigar da dama amma ba a san inda Turji yake ba
  • Ya ce sojojin sama sun far wa ƴan ta'addan tare da haɗin guiwar sojojin ƙasa, suka kasha wasu daga cikinsu yayin da wasu kuma suka arce

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta yi nasarar kashe wasu manyan kwamandojin 'yan bindiga a hare-haren sama da ta kai a jihar Zamfara.

Rundunar sojin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya fitar yau Lahadi.

Kara karanta wannan

An gano halin da hatsabibin dan ta'adda, Aliero ke ciki, ya rikice kan hare haren sojoji

Sojojin Najeriya.
Sojoji sun murkushe yaran Bello Turji da dama a jihar Zamfara Hoto: @HQNigeriaArmy
Asali: Getty Images

A rahoton da Channels TV ta wallafa a ranar 12 ga Janairu, 2025, ya bayyana cewa sojojin sun kai hare-haren ne tare da haɗin gwiwar sojojin ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin sun sheƙe yaran Bello Turji

Duk da cewa ba a bayyana adadin waɗanda aka kashe ba, rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe 'yan bindigar da ke biyayya ga jagoran 'yan bindiga, Bello Turji, da dama.

Akinboyewa ya ce:

"An kashe 'yan bindiga da yawa, yayin da wasu da dama ciki har da wasu manyan kwamandoji, suka ji rauni iri-iri."

Sojoji ba su san wurin da Turji ya ɓuya ba

Ya ƙara da cewa, duk da waɗannan hare-haren da kisan yaransa, har yanzu ba a san inda Bello Turji yake ba.

"Bayan wannan gumurzu mai tsanani, har yanzu ba a san inda Kachallah Bello Turji yake ba, lamarin da yaransa mummunan hali."

Kakakin NAF ya kara da cewa rundunar Operation Fansan Yamma ce ta kai wannan samamen bayan haɗa bayanan sirri daga na'urar leƙen asiri da sa ido.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun tarfa ƴan bindiga, sun hallaka sama da 100

A cewarsa, an ga 'yan bindigan suna gudu zuwa gabashin tsauni a yunƙurin tsira, wanda ya sa aka ci gaba da kai musu hari har aka kashe wasu daga cikinsu.

Mutanen Zamfara sun yi murna

"Wannan nasara ta sa mazauna jihar Zamfara murna da farin ciki kuma sun nuna jin daɗi da godiya ga tasirin aikin sojojin."
"Haka kuma, an ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su, kuma iyalansu sun yi matuƙar farin ciki da dawowar ƴan uwansu," in ji Akinboyewa.

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta jaddada ƙudurinta na ci gaba da aiki tare da sojojin ƙasa domin kawar da duk wani nau'i na laifi a ƙasar.

"Tare za mu yi nasara kan duk wani makiyi da ke barazana ga tsaron yankunan mu da jin daɗin mutanenmu, domin samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasarmu mai albarka," in ji shi.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta yi bayani a kan sace sama da N1bn daga asusun gwamnati

An fargabar sojoji sun kara kuskuren jafe bom

A wani rahoton, kun ji cewa ana fargabar jirgin yaƙin sojojin sama ya yi kuskuren jefa bom a wani kauyen jihar Zamfara ranar Asabar.

Rahoto ya nuna cewa sojojin sun kashe ƴan banga yayin da suka jefa bom a kauyen Kakindawa da ke Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262