Gwamnati Ta Kori Ma'aikatan Shari'a, Ta ba Wasu Alkalan Jigawa Umarnin Yin Murabus
- Hukumar shari’a ta jihar Jigawa ta kori ma’aikanta uku saboda cin amanar aiki da karya dokokin tsarin aikin shari’a
- An bai wa wasu alkalan kotunan shari’a uku shawarar yin murabus saboda sakacin aiki da aikata kuskuren shari’a sau da dama
- Hukumar ta nanata aniyarta na tabbatar da tsabtar tsarin shari’a tare da ladabtar da duk masu aikata rashin gaskiya a Jigawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Hukumar ma’aikatar Shari’a ta jihar Jigawa ta kori ma’aikata uku na shari’a saboda aikata ba daidai ba.
Haka zalika, hukumar ta bai wa wasu alkalan kotunan shari’a uku umarnin yin murabus tare da yin gargadi ga wasu alkalan biyu kan sakacin aiki.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Abbas Wangara, daraktan yada labarai na hukumar ya fitar a ranar Lahadi a Dutse, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta kori ma'aikatan shari'a a Jigawa
A taronta na 178 da aka gudanar ranar 7 ga Janairu, hukumar ta amince da ladabtar da ma’aikatan da aka samu da laifin karya dokokin shari’a.
Sanarwar Abbas Wangara ta ce:
“A rahoton kwamitin bincike daga bangaren babbar kotun jiha, an samu karin bayani kan wasu ma’aikata biyu da suka aikata laifuffuka.
"Ma’aikatan da ake magana a kansu sune Iyal Ibrahim, babban sakataren kotun shari’a a matakin albashi na 08, da Baffa Alhaji, babban sakataren kotun shari’a a matakin albashi na 14.
"An same su da laifin sayar da motoci biyu da aka ajiye a matsayin shaidar kara a babbar kotun tarayya da ke Dutse ba bisa ka’ida ba."
Abbas Wangara ya ce wannan ya saba wa dokokin tsarin aikin shari'a na jihar Jigawa na shekarar 2006, wanda ya tanadi hukunci ga irin wannan laifi.
Saboda haka, hukumar ta yanke hukuncin sallamar su daga aiki bisa tanadin sashe na 41 na dokar aikin shari’a ta Jigawa ta shekarar 2012.
An bukaci alkalai su yi murabus daga aiki
Haka zalika, an sallami Abdu Aujara, babban ma’aikacin kula da kayan aiki, saboda yin sama da fadi da Naira 965,000 na wata ajiyar shari’a da aka yi.
Rahoton kwamitin kararrakin jama’a ya bayyana cewa alkalin kotun shari’a, Adamu Farin-Dutse, ya yi amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba.
Duk da gargadi sau da yawa, an samu Alkali Adamu da aikata ba daidai ba inda aka bukace shi da ya yi murabus cikin makonni biyu.
An kuma bukaci alkalin kotun shari’a, Muhammad Usman, da ya yi murabus saboda laifin bayar da izinin mallakar kadara ba tare da yanke hukunci ba, wanda ya saba wa doka.
Shi ma Alkali Usman Zubair, an same shi da matsaloli a rabon gadon iyali da amincewa da mutane da ba su da alaka da karar, inda aka bukaci ya yi murabus.
An ladabtar da wasu alkalan Jigawa
Alkali Munnir Abdullahi ya samu gargadi kan mayar da batun farar hula zuwa shari’ar laifi tare da nuna bangaranci.
Alkalin kotun majistare, Yakubu Ibrahim, shi ma ya samu gargadi saboda zagin mai kara da amfani da kalmomin cin zarafi yayin shari’a.
Abbas Wangara ya tabbatar da cewa matakan ladabtarwa na nufin tabbatar da tsaftar tsarin shari’a tare da inganta ka’idoji da nagarta a aikace.
Majalisa ta amince da karin albashin alkalai
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta amince da kudirin dokar karin albashi ga Babban Joji na kasa da alkalan kotunan Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da bukatar, inda idan ya rattaba hannu, Babban Joji zai samu albashi kusan N60m a shekara.
Asali: Legit.ng