Auren Jinsi: Tinubu Ya Kawo Sabuwar Doka ga Sojoji kan Luwadi da Madigo, Ya Yi Gargadi

Auren Jinsi: Tinubu Ya Kawo Sabuwar Doka ga Sojoji kan Luwadi da Madigo, Ya Yi Gargadi

  • Jami'an sojoji a Najeriya za su fuskanci hukunci mai tsanani bayan amincewa da dokar hana madigo da luwadi a tsakaninsu
  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sashi na 26 na sabuwar dokar da ta hana sojoji auren jinsi da lamarin yan daudu
  • Dokar ta kuma haramta wa sojoji yin zane a jiki (tattoo) da shaye-shaye, da duk wani hali da zai kawo abin kunya a bainar jama’a
  • Kasar Najeriya tana da dokar da ke hukunta yan luwadi da madigo, duk da korafe-korafen wariya daga mambobin kungiyar a fadin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a sabuwar dokar da ta haramta madigo da luwadi a tsakanin sojoji.

Tinubu ya amince da sashi na 26 na sabuwar dokar sojoji da aka yi mata fasali wacce haramta wa sojojin Najeriya shiga ayyukan kungiyar da saka kayan mata.

Kara karanta wannan

An gano halin da hatsabibin dan ta'adda, Aliero ke ciki, ya rikice kan hare haren sojoji

Tinubu ya haramta wa sojoji auren jinsi
Bola Tinubu ya amince da haramta auren jinsi tsakanin sojoji a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Yadda yarjejeniyar Samoa ta jawo ka-ce-na-ce

Shugaban ya sanya hannu kan dokar a ranar 16 ga watan Disambar 2025, kamar yadda rahoton The Guardian ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Bola Tinubu ta sanya hannu a yarjejeniyar Samoa da ake ganin na da alaka da halasta auren jinsi.

Hakan ya jawo ka-ce-na-ce a fadin Najeriya musamman Arewacin kasar da ake ganin ya saba addini da kuma al'adun al'umma.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar cewa akwai auren jinsi a ciki inda ta ce ta sanya hannu ne a wani bangare na inganta harkokin kasuwanci.

An haramta wa sojoji luwadi, madigo

Wannan doka ta kuma hana sojoji yin zane a jikinsu (tattoo) da shaye-shaye da duk wani hali da shafi yan daudu.

"Jami’i ba zai yi luwadi, madigo, ko wasu dabi’u marasa kyau ba, ya kuma haramta shiga ayyukan kungiyar ko saka kayan mata."

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun tarfa ƴan bindiga, sun hallaka sama da 100

"Jami’i bai kamata ya yi zane a jikinsa ko bula sassan jikinsa ba, bai kamata ya yi shaye-shaye ko wani hali da zai jawo masa kunya ba."

- Cewar wasu sassan dokar

Yadda ake ganin yan daudu a al'adance

A Najeriya, ana hukunta masu luwadi da madigo kuma ana kallon ayyukan kungiyar a matsayin abin da ya saba wa al’ada, Punch ta ruwaito.

Sai dai mambobin kungiyar yan daudu da masu ayyukan luwadi da madigo suna korafi kan wariya da cin zarafinsu da ake yi kan haka.

Kungiya ta bukaci halasta auren jinsi a Najeriya

Kun ji cewa ana ci gaba da fafutukar dakile yunkurin tabbatar da barin masu son auren jinsi su wala a Najeriya, wata kungiya ta bullo da sabon batu.

Kungiyar ta Creative Africa Initiative ta rubuta wasika da tambarin ma'aikatar ilimi ta na neman a bayar da damar tattauna batun auren jinsi.

Tuni Gwamnatin Tarayya tarayya ta barranta kanta da wannan lamari, inda ta ce ya saba da addini, al'ada da ra'ayin akasarin 'yan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.