An Gano Halin da Hatsabibin Dan Ta'adda, Aliero ke ciki, Ya Rikice kan Hare Haren Sojoji
- Shugaban 'yan bindiga Ado Aliero, wanda ya addabi Zamfara, yanzu yana wasan boye da sojoji saboda karin matsin da rundunar ke yi wa 'yan ta'adda
- Rundunar tsaro ta samu nasarori ta hanyar kai farmaki da dabaru kan 'yan bindiga a yankunan Gabas da Yammacin Tsafe a jihar Zamfara
- Dan uwansa, Dan Isihu, wanda ake zargi da kashe-kashe da dama, ya tsere bayan haduwa da jami'an tsaro a hanyar Kyaware
- Wannan bai rasa nasaba da kokarin jami'an tsaro a kullum wurin ganin an kakkabe yan ta'adda a yankunan Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Tsafe, Zamfara - Hatsabibi kuma fitaccen shugaban 'yan bindiga, Ado Aliero ya rasa inda zai saka kansa saboda hare-haren sojoji.
Aliero wanda ya dade yana tayar da hankula da kashe-kashe a Zamfara da kewayenta, yanzu yana cikin tsananin tsoro.
Yadda Sojoji ke samu nasarar kan yan ta'adda
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar hakan na faruwa ne sakamakon karin matsin lamba daga sojoji suke yi a yankunan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa sojojin na gudanar da farmakin a yankunan da 'yan bindiga suka addaba musamman a Arewa maso Yamma.
Rundunar tsaro ta tabbatar da samun nasarori ta hanyar kai hare-hare da dabarun kakkabe 'yan bindiga a yankunan Gabas da Yammacin Tsafe.
Dan ta'adda, Aliero ya shiga halin matsi
Rahotanni daga majiya mai tushe sun bayyana cewa Aliero ya koma buya a wani kauyen karkarar Gabashin Tsafe da ake kira Asaula.
An ce Ado Aliero yana ta canza wuraren boyewa don gudun kada ya fada hannun jami’an tsaro da ke matsa wa 'yan bindiga lamba.
A gefe guda, dan uwansa, Dan Isihu, wanda aka dora alhakin kashe-kashe da dama a wannan yanki, ya tsere daga hannun sojoji.
An ruwaito cewa Dan Isihu ya yi kokarin tserewa ta hanyar ketare wani kogi bayan gamuwa da jami'an tsaro a hanyar Kyaware.
Wasu al'umma sun nemi alfarma wurin sojoji
Sai dai kuma, duk da tserewar tasa, sojoji sun bi shi cikin tsananin kwarewa don tabbatar da sake cafke shi kafin ya tsallaka wani yankin.
Wannan kokari na sojoji ya janyo karancin yawan kai hare-haren 'yan bindiga a yankunan da suka fi fama da wannan matsala.
Mazauna yankunan suna bayyana jin dadinsu da kuma burin ganin an kawo karshen 'yan bindiga gaba daya a yankin Tsafe da kewayenta.
Bello Turji ya rikice kan jarin sojoji
A baya, kun ji cewa an gano rikakken dan ta'adda Bello Turji da yaransa sun kwana suna dasa wasu abubuwa a kusa da duwatsun Fakai da Manawa don kare kansu daga hare-hare.
Duwatsun Fakai da Manawa sun zama mafaka ga Turji da tawagarsa duk lokacin da suka ji barazanar farmaki daga jiragen soja ko idan suna shawagi.
Yan tawagar sun tsara wannan aikin ne don kare kansu yayin da suke tsoron hare-haren sojoji musamman a yanzu da ake musu barazana.
Asali: Legit.ng