Jami'an Tsaro Sun Samu Nasara, Sun Sheke Gawurtaccen Shugaban 'Yan Bindiga
- Jami'an tsaro sun samu nasarar rage mugun iri a jihar Katsina bayan sun hallaka wani gawurtaccen shugaban ƴan bindiga mai suna Baƙo Baƙo
- Masu aikin samar da tsaron sun hallaka shugaban ƴan bindigan ne bayan sun kai farmaki cikin ƙwarewa a sansaninsa da ke ƙaramar hukumar Batsari
- Mutanen yankin sun nuna farin cikinsu kan namijin ƙoƙarin da jami'an tsaron suka yi wajen raba su da Baƙo Baƙo wanda ya daɗe yana addabarsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka wani gawurtaccen shugaban ƴan bindiga, Baƙo Baƙo a jihar Katsina.
Jami'an tsaron sun hallaka shugaban ƴan bindigan ne tare da tawagar mayaƙansa a dazuzzukan ƙaramar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta rahoto cewa an samu nasarar hallaka shugaban ƴan bindigan ne bayan farmakin haɗin gwiwa da aka kai a maɓoyarsa.
Jami'an tsaro sun farmaki shugaban ƴan bindiga
Farmakin wanda aka gudanar da yammacin rana, ya haɗa jami'an sojojin Najeriya, ƴan Sanda, hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC), da kuma ƴan sa-kai.
Jami'an tsaro sun daɗe suna farautar Baƙo Baƙo, wanda ya shahara wajen jagorantar hare-haren ta'addanci da sace-sacen mutane a faɗin jihar Katsina.
Kashe shi wata babbar nasara ce a ci gaba da yaƙi da ƴan bindiga da ake yi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Bisa ga bayanan da suka fito daga majiyoyin tsaro, an gudanar da farmakin ne cikin tsari domin ganin an tabbatar da zaman lafiya da kuma tsaro.
Sojoji sun kutsa sansanin ɗan bindigan da yamma inda aka yi musayar wuta da mayaƙansa.
Fafatawar ta kai ga nasarar fatattakar Baƙo Baƙo da tawagarsa ta hanyar amfani da makaman zamani da kuma ƙwarewar da jami’an tsaro suka nuna.
Mutane sun yi farin cikin kashe 'dan bindigan
Wannan nasarar ta kawo farin ciki ga mazauna ƙaramar Hukumar Batsari, waɗanda suka nuna godiyarsu ga jami’an tsaro kan jarumtaka da ƙwazon da suka nuna.
Wani shugaban al’umma a yankin ya ce kisan Baƙo Baƙo babbar nasara ce a gare su.
"Wannan babbar nasara ce ga al’ummominmu. Muna matuƙar godiya bisa ƙoƙari da sadaukarwar sojoji wajen dawo da zaman lafiya a yankinmu."
- Shugaban al'umma
Wannan nasara ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwar hukumomin tsaro wajen yaƙi da rashin tsaro.
Jami’an tsaro sun sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuffuka, domin tabbatar da cewa Katsina ta samu cikakken tsaro.
Jami'an tsaro sun yi abin a yaba
Muhammad Kamal ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da jami'an tsaron suka samu abin a yaba ne matuƙa.
"Gaskiya wannan abin jin daɗi ne sosai domin an rage mugum iri a cikin al'umma. Muna yi wa jami'an tsaro addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara kan miyagu."
"muna kira ga gwamnati da ta ci gaba da ba su dukkanin goyon bayan da suke buƙata domin fatattakar ƴan bindiga."
- Muhammad Kamal
Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan Katsina sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai kan matafiya.
Jami'an ƴan sandan sun ragargaji ƴan bindigan tare da kuɓutar da fasinjojin da suka yi garkuwa da su a kan titin hanyar Funtua zuwa Gusau.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


