Gwamnan Kano Ya Gwangwaje Wata Hadimarsa da Kyautar Gidan N19m, Ta Karbi Mabudi

Gwamnan Kano Ya Gwangwaje Wata Hadimarsa da Kyautar Gidan N19m, Ta Karbi Mabudi

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sayawa wata hadimarsa gidan Naira miliyan 19, tare da kashe miliyan ɗaya wajen gyara shi
  • Hajiya Hauwa Muhammad, mai tallafa wa gwamna a harkokin mata, ta samu kyautar gidan ne saboda kwazonta a cigaban Kano
  • Takardar kyautar gidan na ɗauke da sa hannun Abba da Hajiya Hauwa, tare da fatan gidan zai zama masaukin farin ciki ga iyalanta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gwangwaje daya daga cikin masu tallafa masa, Hajiya Hauwa Muhammad da kyautar gidan Naira miliyan 19.

Hajiya Hauwa Muhammad ita ce mai tallafawa Abba ta fuskar harkokin mata.

Gwamnan Kano ya yi magana yayin da ya ba wata hadimarsa kyautar gidan N19m
Gwamnan Kano ya ba mai tallafa masa kan harkokin mata kyautar gidan N19m. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Amir Abdullahi Kima
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da wani Salisu Yahaya Hotoro ya fitar a shafinsa na Facebook dauke da takardar kyautar gidan, Gwamna Abba ya kuma gyara gidan da kayan Naira miliyan daya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya shiga jimami, hadiminsa ya rasu awanni bayan nadinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya ba hadimarsa kyautar gidan N19m

Da Legit Hausa ta karanta takardar, ta fahimci cewa sakataren kashin kai na gwamnan Kano (PPS), Dakta Sani Danjuma ne ya sanyawa takardar hannu.

Har ila yau, akwai sa hannun gwamnan na Kano, Abba Kabir Yusuf a matsayin mai bayarwa da kuma sa hannun Hajiya Hauwa a matsayin mai karba.

Gwamnan Kano ya ce bayan sayawa 'yar gwagwarmayar gidan na Naira miliyan 19, ya kuma kashe Naira miliyan daya wajen sanya masa kayan alatu.

Abin da takardar bayar da gidan ta kunsa

A jikin takardar bayar da gidan, Dakta Sani Danjuma ya ce:

"Cike da farin ciki nake sanar da ke cewa mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya saya maki gida tare da sanya maki kaya a ciki domin nuna godiya ga kwazonki.
"Gidan dai an saye shi ne a kan Naira miliyan 19, kuma an kashe masa Naira miliyan daya wajen yi masa gyare-gyare da kawayata shi.

Kara karanta wannan

Tinubu: Martanin 'yan Najeriya kan 'nasihar' gwamnan Bauchi ga Sheikh Jingir

"Wannan kyautar, wata hanya ce da mai girma gwamnan ke amfani da ita wajen sakawa jajurtattun mutanen da ke aiki ba dare ba rana wajen ci gaban jihar Kano.

Gwamna ya mika takardu da makullan gidan

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Gwamnan yana fatan cewa wannan gidan zai zama wani matsugunni mai tsaro da kuma zama muhallin da zai sanya farin ciki a gare ke da iyalanki.
"A hade da wannan takardar, za ki samu malli da takardun gidan wadanda aka riga aka sanyawa hannu a hukumance domin tabbatar da cewa yanzu ya zama mallakinki."

Hadimin Abba da aka ba mukami ya rasu

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alhinin rasuwar Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure, wanda ya rasu ranar Laraba a ƙasar Masar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanar da rasuwar Injiniya Bunkure, sabon mai ba da shawara kan ayyuka.

Kara karanta wannan

Dan Bilki Kwamanda: Abba ya hana ni zuwa aikin hajji duk da taimakon Kashim Shettima

Gwamna Yusuf ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi kuma ya yi addu’a Allah ya ji ƙan mamacin ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jure rashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.