Tinubu Ya Ware Biliyoyin Naira kan Jiragen Shugaban Kasa a 2025
- Gwamnatin Tarayya ta shirya kashe Naira biliyan 55 ga rukunin jiragen shugaban kasa a kasafin kudin shekarar 2025
- Rahotanni sun nuna jam’iyyun adawa sun bayyana cewa kashe wannan kudin ya saba wa bukatun talakawan Najeriya a halin yanzu
- Kungiyoyin fararen hula da wasu masu sharhi sun bukaci gwamnatin tarayya ta sake tunani kan lamarin saboda halin da ake ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fuskanci suka daga jam’iyyun adawa da masu sharhi kan shirin kashe Naira biliyan 55 da aka ware ga jiragen shugaban kasa a kasafin 2025.
Tanadin kudin na kunshe ne cikin kasafin kudin 2025 da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gabatar wa Majalisar Dokoki domin tantancewa da amincewa.
Punch ta rahoto cewa wasu 'yan Najeriya sun yi Allah wadai da matakin, suna mai cewa ya nuna rashin kula da matsalolin da ke damun talakawa a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan adawa sun yi martani mai zafi
Shugaban jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso Yamma, Kamorudeen Ajisafe, ya tambayi ko akwai wani sabon jirgi da gwamnati ke shirin saye, yana mai cewa babu fa'idar kashe kudin.
A bangaren jam’iyyar LP, mai magana da yawun jam’iyyar, Abayomi Arabambi, ya bayyana matakin a matsayin rashin tausayi da rashin sanin ciwon jama’a.
Abayomi Arabambi ya ce:
“Kashe irin wannan kudi kan jiragen shugaban kasa a yayin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke cikin talauci babbar kuskure ne.
"Wannan lamari ya nuna yadda gwamnati ba ta damu da rage talauci ko rashin daidaito tsakanin 'yan kasa ba.”
Arabambi ya kara da cewa wannan mataki ya saba wa alkawarin rage kashe-kashen banza da gwamnati ta yi wa jama’a.
Martanin kungiyoyin fararen hula
Shugaban kungiyar CACOL, Debo Adeniran, ya bayyana cewa kashe kudi da ba a kan muhimman abubuwa ba babban abin kunya ne ga Najeriya.
Debo Adeniran ya ce,
“Gwamnatin da ke kuka kan rashin kudi ita ce kuma ke kashe biliyoyin Naira kan abubuwan da ba su da mahimmanci. Lokaci ya yi da za a fara fifita bukatun jama’a a kan na gwamnati.”
Adeniran ya yi kira ga al’umma su dage wajen ganin shugabanni sun fuskanci matsalolin da ke addabar kasar maimakon batar da kudin jama’a.
Ya kara da cewa idan har wannan lamari ya ci gaba, babu abin da zai sauya face kara gurguntar da ci gaban kasar nan.
Ra’ayin jama’a kan jiragen shugaban kasa
Injiniya Olakunle Aina ya bayyana takaicinsa kan yadda gwamnati ke kashe kudi kan jiragen shugabanta, yana mai cewa:
“Ko ba ni injiniyan jirgin sama ba ne, na san wannan kudi ya yi yawa domin kawai a kashe shi kan tafiye-tafiye.
"Idan shugabanni za su rage almubazzaranci, kudin za su yi amfani wajen tallafawa talakawa.”
Aina ya kara da cewa kashe irin wannan kudi yayin da miliyoyin mutane ke fama da yunwa ya nuna rashin sanin halin da kasar ke ciki daga bangaren shugabanni.
A nata bangaren, wata ‘yar kasuwa ta bayyana cewa kashe irin wannan kudi yana jefa talakawa cikin damuwa.
'Yar kasuwar ta ce,
“Ina jin kunyar jin labarin cewa za a kashe biliyan 55 kan jiragen shugaban kasa, alhali ni na shekara guda ina tara N150,000.
"Wannan lamari ya kamata ya ja hankalin shugabanni su gane halin da talakawa ke ciki.”
Gwamna ya kai karar Tinubu wajen Jingir
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Bauchi ya tura sako ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta hanyar Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Sanata Bala Mohammed ya koka kan cewa ba su jin dadin yadda Tinubu ke jagorantar kasar nan ba musamman kan zargin cewa ba a girmama ra'ayin jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng