Gwamna Ya Canza Sunan Jami'a, Ya Raɗa Mata 'Jami'ar Kashim Ibrahim'
- Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya amince da sauya sunan jami'ar jihar zuwa Jami'ar Kashim Ibrahim
- Zulum ya amince da hakan ne a taron majalisar zartarwa ta jiha (SEC) na farko a 2025 wanda ya gudanar ranar Litinin a fadar gwamnatinsa
- Kwamishinan yaɗa labarai na Borno, Farfesa Usman Tar ya ce majalisar ta amince da sauya sunayen tituna da yi wa gidaje lambobi a birane
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno - Majalisar zartarwa ta Borno ta amince da sauya sunan jami’ar jihar zuwa 'Jami’ar Kashim Ibrahim' a matsayin girmamawa ga gwamnan farko na tsohuwar jihar Arewacin Najeriya.
An cimma wannan matsaya ne a taron farko na majalisar zartarwa ta jihar (SEC) a 2025, wanda Gwamna Babagana Umara Zulum ya jagoranta.
Taron, wanda ya gudana a daren Litinin a dakin taro na fadar gwamnatin Borno da ke Maiduguri, ya shafe sama da sa’o’i shida, kamar yadda Leadership ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum ya jagoranci taron SEC
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Usman Tar, ya bayyana cewa Majalisar ta duba takardu guda 42.
Ya ce SEC ƙarƙashin Gwamna Zulum ta kuma yi waiwaye adon tafiya kan ayyukan da gwamnati ta gudanar a shekarar da ta gabata, da kuma hasashen ayyukan 2025.
Farfesa Tar ya ƙara da cewa sauya sunan jami’ar jihar zai tabbata ne bayan bin ka’idojin dokoki tare da sanar da hukumomin da suka dace kamar dai ma’aikatar ilimi.
Gwamna ya sauya sunan jami'ar Borno
"Majalisar zartarwa ta amince da sauya sunan jami’ar jihar Borno zuwa Jami'ar Kashim Ibrahim, Maiduguri. Hakan zai tabbata ne bayan majalisar dokoki ta amince ta gyara dokar da ta kafa jami'ar.
"Haka nan an dorawa ma’aikatar ilimi nauyin bin ƙa'idoji ta hanyar sanar da hukumomin da abin ya shafa kamar hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC), hukumar shirya jarrabawar shiga Jami’a (JAMB) da sauransu."
- Farfesa Usman Tar.
Gwamnatin Borno za ta canza sunayen tituna
Kwamishinan ya ƙara da cewa an kuma amince da raɗawa hanyoyi sunaye da sake lambobin gidaje a Maiduguri da sauran biranen jihar Borno.
Farfesa Usman ya ce wannan wani ɓangare ne na shirin sabunta birane da gwamnatin Zulum ta ɓullo da shi, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ya ce birnin Maiduguri na ƙara ci gaba sosai, an yi sababbin gine-gine da hanyoyin da ya kamata a raɗa masu sunayen da suka dace
Bisa haka kwamishinan yaɗa labarai ya ce gwamnatin Borno ta umarci hukumomin da ke da alhaki su zauna da masu ruwa da tsaki domin yanke sunan da ya dace da kowane titi ko layi.
Gwamna Zulum ya sa hannu a kasafin 2025
Kun ji cewa Gwamna Babagana Umaru Zulum ya rattaɓa hannu kan kudirin dokar kasafin kudin 2025 wanda zai laƙume N615.857bn.
Hakan ya biyo bayan amincewar majalisar dokokin jihar Borno bayan ta yi ƙarin kudi N31.1bn a kan adaɗin da gwamnan ya gabatar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng