Zulum Ya Yi Muhimmin Naɗi yayin da Ya Rattaba Hannu kan Kasafin N615.8bn
- Gwamna Babagana Zulum ya rattaba hannu kan kasafin jihar Borno na 2025, wanda aka yi masa karin N31.1bn zuwa N615.857bn
- Kakakin majalisar jihar ne ya gabatarwa Zulum da kasafin a Maiduguri, inda aka yaba wa majalisar kan amincewarsu cikin gaggawa
- Zulum ya sanar da nadin Dakta Mustapha Mallumbe a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata, don maye gurbin Hussaini Marte
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - A ranar Litinin, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya rattaba hannu kan kasafin 2025 na Naira biliyan 615.857.
Gwamna Zulum ya rattaba hannu kan kasafin ne bayan kakakin majalisar dokokin jihar, Abdulkarim Lawan, ya gabatar da kudurin a Maiduguri.
Zulum ya rattaba hannu kan kasafin 2025
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Zulum ya sanya hannu kan kasafin yayin da aka kara Naira biliyan 31.1 a kan wanda aka gabatar tun da fari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa a ranar 9 ga Disamba, 2024, gwamnan ya gabatar da kasafin Naira biliyan 584.76 mai taken “Kasafin farfadowa da ci gaba.”
Sai dai bayan gyare-gyare da majalisar dokokin jihar ta yi, gwamnatin jihar ta kara Naira biliyan 31.1, wanda ya sa kasafin kudin ya koma Naira biliyan 615.857.
Zulum ya gargadi shugabannin ma'aikatu
Gwamnan ya jinjinawa majalisar dokokin saboda amincewa da kasafin a kankanin lokaci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
An ce Gwamna Zulum ya kuma gargadi shugabannin ma’aikatu da hukumomi da su bi dokokin kasafin yadda ya kamata.
“Dole ne mu yaba wa shugabanni da ‘yan majalisar dokokin jihar saboda hangen nesa da hadin kan da suka nuna,” in ji Zulum.
Majalisa ta fadi dalilin gyaran kasafi
Zulum ya sake tabbatar da kudurinsa na cika alkawurran da ya dauka yayin yakin neman zaben shekarar 2023.
Tun da fari, kakakin majalisar dokin Borni, Rt. Hon. Lawan ya yaba wa Zulum kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru shida.
Rt. Hon. Lawan ya bayyana cewa majalisar ta yi gyare-gyare kan kasafin da gwamnan ya gabatar domin magance matsalolin al’umma.
2025: Zulum ya jagorancin zaman SEC
Bayan haka, Zulum ya jagoranci zaman farko na majalisar zartarwa ta shekara bayan rattaba hannu kan kasafin.
Ya nuna godiyarsa ga mataimakinsa, Alhaji Umar Kadafur, sakataren gwamnati, Dakta Bukar Tijjani, shugabannin ma’aikatu, da kafafen yada labarai kan gudunmuwarsu a ci gaban al’umma.
Zulum ya sake ba kwamishina mukami
Haka kuma, Zulum ya nada kwamishinan kasafi da tsare-tsarn tattalin arziki, Dakta Mustapha Mallumbe a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.
An ruwaito cewa nadin Mallumbe ya biyo bayan gurbin da aka samu na tafiyar shugaban ma’aikata, Farfesa Hussaini Marte, wanda ke samun sauki a yanzu.
Zulum ya fara biyan sabon albashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Babagana Zulum ya fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a jihar Borno, wanda aka fara aiwatarwa.
Kwamishinan kasafi ya ce ma'aikata sun fara samun sabon albashi, ya kuma yaba wa Zulum bisa goyon bayan da ya bai wa kwamitin albashi.
Asali: Legit.ng