Bayan Barazanar Bello Turji, Sojoji Sun Kashe Ɗan Ta'addan da Aka Daɗe Ana Nema
- Jami’an tsaro sun kashe sanannen ɗan ta’adda, Sani Rusu, wanda aka dade ana zargin shi da kai hare-hare a yankin gabashin Tsafe
- Duk da nasarar da aka samu, wani dillalin ƙwayoyi, Shamsu Danmali, ya tsere yayin harin, amma sojoji na cigaba da neman sa
- Wannan samame ya nuna irin manyan matakan da sojoji suke dauka na tabbatar da zaman lafiya a Zamfara wanda ya samu yabo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara- Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a wani samame da suka kai Bamamu, karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.
An ce jami'an tsaron sun samu nasarar kashe sanannen ɗan ta’adda, Sani Rusu wanda aka dade ana nemansa.
Sojoji sun kashe dan bindiga Sani Rusu
Rahoton da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X ya nuna cewa sojoji sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri kan wurin da Sani Rusu ke ɓoye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sani Rusu, ɗan ta’addar Fulani ne wanda ake zargin shi da kai hare-hare da dama a yankin gabashin Tsafe, wanda ya addabi al’umma.
Bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaro sun gudanar da samame cikin gaggawa, wanda ya kai ga kashe shi.
Zamfara: Sojoji na neman abokin Sani Rusu
Duk da haka, wani da ake zargin dillalin miyagun ƙwayoyi ne kuma na hannun daman Sani Rusu mai suna Shamsu Danmali, ya tsere yayin samamen..
Hukumomin tsaro suna ci gaba da ƙoƙarin kamo Shamsu Danmali, wanda ake zargin yana taimaka wa ayyukan ta’addanci a yankin.
Mazauna yankin Tsafe sun sha fama da hare-haren ƴan ta’adda, wanda ya haifar da matsalar tsaro da ta tsananta a shekarun baya.
An jinjinawa sojoji kan kashe 'yan ta'adda
Wannan nasarar da aka samu tana ɗauke da muhimmiyar rawa wajen dawo da zaman lafiya da tsaron rayuka a yankin.
Samamen ya bayyana himmar jami’an tsaro wajen ƙwatar yankunan da ƴan ta’adda ke addaba da tabbatar da zaman lafiya.
Mazauna yankin sun yaba da nasarar da jami’an tsaro suka samu, suna masu fata a ci gaba da kai irin waɗannan hare-hare na musamman.
Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa za su ci gaba da amfani da bayanan sirri don kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara baki ɗaya.
Bello Turji ya yi barazana bayan kama abokinsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa hatsabibin ɗan ta'adda, Bello Turji, ya yi barazana mai tsanani bayan cafke abokin aikinsa na kusa, Bako Wurgi, a yankin Sokoto.
An ce Wurgi na da matuƙar muhimmanci wajen tattaunawa da karɓar kuɗin fansa, yana kula da yankunan Isa, Sabon Birni, da Shinkafi.
Cafke Wurgi ya fusata Turji ƙwarai, lamarin da ya haifar da tsoro a tsakanin al'ummar yankin da hukumomi na Sokoto da Zamfara.
Bello Turji ya shaida wa shugabannin al'umma cewa zai kai hare-hare idan ba a gaggauta sakin abokin nasa, Wurgi, ba.
Asali: Legit.ng