An kama hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a jallo a cikin coci a Legas

An kama hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a jallo a cikin coci a Legas

  • Jami'an NDLEA sun kama wani dillalin miyagun kwayoyi a wani coci da ke Ojudu a Legas
  • Mr Femi Babafemi, kakakin NDLEA ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar
  • An kama Stephen Ikeanyionu ne bayan bincike kan miyagun kwayoyin da aka kama a filin tashin jirage na Legas

Jami'an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA ta kama wani da ake zargin dillalin miyagun kwayoyi ne da ya yi yunkurin fitar da hodar ibliss wato koken da hero*n da ganyen wiwi mai nauyin kilo gram 69.65kg zuwa Birtaniya.

The Cable ta ruwaito cewa mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani coci da ke Legas.

An kama dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa jallo a cikin coci a Legas
Jami'an NDLEA tare da wasu miyagun kwayoyi da suka kama. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ya ce an gano wanda ake zargin kuma ake nema ruwa a jallo, Stephen Afam Ikeanyionu, a wani coci da ke unguwar Ojodu a Legas.

The Guardian ta ruwaito cewa an kama miyagun kwayoyin ne a filin tashi da saukan jirage na Legas a ranar Alhamis kuma aka gano Ikeanyionwu ne ya mallake su.

Yadda aka gano Stephen Ikeanyionu

Sanarwar ta ce:

"Jami'an NDLEA sun gano dillalin miyagun kwayoyi da ake nema ruwa a jallo, Stephen Afam Ikeanyionwu, a ranar Lahadi, 15 ga watan Agustan 2021, a wani coci da ke layin Mike Ajari, Ojodu Berger, inda suka kama shi bayan ya fito daga addu'ar lahadi."
"An kama shi ne bayan gano wasu haramtattun miyagun kwayoyi masu nauyin 69.65kg da za su tafi Birtaniya ta filin tashin jiragen sama na Legas a ranar Alhamis, 12 ga watan Agustan 2021. Wani kamfanin jigilar kaya ne aka bawa jigilar kayan, kamfanin kuma ta bawa wani direba ya kai wurin karbar kaya a NAHCO.

"Bayan kama direban, an gudanar da bincike inda daga bisani aka gano ainihin mai kayan, Stephen Afam Ikeanyionwu, kuma aka kama shi kwana uku bayan kai sumame."

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

A wani labarin daban, kun ji cewa kungiyoyi biyu na wasu shu’uman ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda harbe-harbe ya barke tsakaninsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rikicin ya yi sanadiyyar halakar mutane 9 a cikinsu kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel