Maganar Haraji Ta Dawo, Tinubu Ya Nemo Hanyar Lallaba Manyan Arewa, Gwamna Ya Kafe

Maganar Haraji Ta Dawo, Tinubu Ya Nemo Hanyar Lallaba Manyan Arewa, Gwamna Ya Kafe

  • Shugaba Bola Tinubu ya fara tura wakilai zuwa wurin manyan Arewa don samun goyon baya kan kudirin gyaran haraji
  • Gwamnonin Arewa sun jaddada matsayinsu na kin amincewa da kudirin gyaran haraji duk da kokarin Tinubu
  • Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammad Yahaya ya ce ba za su janye matsayinsu ba sai an sake nazarin kudirin gyaran harajin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya neman hanyoyin wasu saboda shawo kan manyan Arewa game da kudirin gyaran haraji.

An tabbatar da cewa Tinubu ya shirya tura wakilai na musamman domin shawo kan manyan yankin game da kudirin harajin.

Tinubu ya fara neman hanyar shawo kan manyan Arewa kan kudirin haraji
Bola Tinubu ya fara tura wakilai domin lallaba yan Arewa kan kudirin haraji. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Wace matsaya gwamnonin Arewa ke kanta?

Punch ta ce wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Tinubu yana tuntubar wasu daga manyan 'yan siyasar Arewa domin samun goyon bayansu.

Kara karanta wannan

Tinubu na ganin sabuwar matsala daga Arewa, dattawa sun ƙi yarda da gyaran haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa bayan gwamnonin Arewa sun dage cewa ba za su sauya matsayarsu ba kan kudirin.

Gwamnan Gombe kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Muhammad Yahaya, ya tabbatar da cewa suna nan kan matsayinsu na kin amincewa da kudirin.

Mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya ce gwamnonin Arewa sun bayyana matsayarsu kuma ba su sauya ba.

“Wannan matsayar ba ta sauya ba, gwamna ba zai zama mai sauya magana ba, domin yana shugabantar gwamnoni daga APC da PDP."

- Ismaila Uba Misilli

Dabarun da Tinubu ya fara kan kudirin haraji

Wani jami'in gwamnati, wanda ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da cewa Tinubu na tuntubar wasu manyan yan Arewa, cewar TheCable.

“Yana amfani da hanyoyi daban-daban da suke a gare shi don tabbatar da an gyara muhimman bangarorin kudirin."

- Cewar majiyar

Dattawan Arewa sun sake taso Tinubu a gaba

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani, an gano mai zuga gwamna ya yi wa Bola Tinubu 'rashin kunya'

Kun ji cewa Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta bukaci Shugaban Bola Tinubu da ya janye kudurorin gyaran haraji da ya gabatarwa majalisa.

NEF ta zargi gwamnatin Tinubu da yin kama-karya wajen tsara kudurorin da kuma hana mutane furta ra'ayoyinsu kan dokokin.

Dattawan Arewa sun bukaci Tinubu ya dakatar da batun karin harajin VAT har sai an tabbatar da farfadowar tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.