Farfesoshin Jami’ar ABU Zaria Sun Fito da Illolin da ke cikin Kudirin Gyaran Haraji
- Masanan da ke cibiyar CEDERT sun yi binciken tasirin kudirorin gyaran haraji ta fuskar tattali da zamantakewa
- Farfesa Abubakar Siddique Muhammad da Farfesa Aliyu Sanusi Rafindadi sun yi nazari a kan kudirorin gwamnatin
- A karshe sun fadi matsalolin da za a fuskanta idan aka fito da sabuwar dokar tare da ba gwamnati wasu shawarwari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Cibiyar CEDERT a Zariya ta yi bincike da nazari na musamman game da kudirorin gyaran haraji da gwamnati ta bijiro da shi.
Farfesa Abubakar Siddique Muhammad da Farfesa Aliyu Sanusi Rafindadi da ke ABU sun duba kudirorin ta fuskar tattalin arziki da siyasa.
Garajen ganin kudirin haraji ya samu shiga
Tun farko cibiyar ta ce akwai alamun tambaya ganin yadda gwamnatin tarayya ta ke gaggawa domin kudirin ya zama doka a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da al’umma ke rage yarda da shugabanninsu, CEDERT ta ba da shawarar a tsaya a tattauna da kyau domin a karbi kudirin.
Tasirin dokar haraji a kundin tsarin mulki
Kwanaki majalisar NEC ta bukaci a janye kudirin amma gwamnati ta yi watsi da batun, ana zargin wannan ya nuna halin ko in kula.
Idan aka yi na’am da kudirin masanan sun tsorata cewa an kama hanyar yi wa manufofin tattalin arziki da na siyasa garambawul.
Bayan gyare-gyare da kudirin zai tilasta a yi, dole sai an yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin an shiga hurumin RMFAC.
Yadda kudirin zai kashe hukumomin tarayya
A wata wallafa da aka fitar mai shafuka 53, farfesoshin sun ce kudirin haraji na 2024 zai yi sanadiyyar rage karfin hukumar TETFund.
Soke TETFund ko rage mata karfi yana nufin za a rungumi tsarin NELFund, watau an koma dogara da bashi wajen yin karatun jami’a.
Ba a nan kadai abin ya tsaya ba, ana zargin taba hanyar samun kudin NASENI da NITDA zai jawo gwamnatin tarayya ta kori ma’aikata.
Kalubale wajen rabon haraji VAT a jihohi
A bangaren tattalin arziki, karin harajin VAT daga 7.5% har a kai 15% zai jawo tashin farashin kaya a lokacin da ake fama da tsadar kaya.
Takardar ta dage cewa kudirin zai fifita Legas, Ogun, Ribas, Kano da Abuja da suka zama hedikwatocin manyan kamfanoni a kasar nan.
Ko da an canza tsarin rabon VAT daga hedikwata zuwa inda aka yi amfani da kaya a karshe, masanan sun ce sam ba za a iya gane hakan ba.
Kamfanoni da yawa ba za su iya gane jihohin da aka yi amfani da kayansu ba, don haka fahimtar yadda za a yi kason zai ba da wahala.
Muddin aka canza salon haraji kuwa, malaman jami’ar sun ce an bude kofar jawo masana da fasahar zamani da za su tsawwalawa mutane.
Farfesa Siddique da Farfesa Rafindadi sun ce akwai alamun yaudara da ake ikirarin kason Legas zai ragu idan za a raba kason harajin VAT.
Kira ga gwamnatin Bola Tinubu
Sannan sun ba da shawarar a tattauna da jama’a, a daina maida lamarin kamar yaki tsakanin Kudu da Arewacin Najeriya ko makamancin haka.
A karshe takardar ta nemi a bi majalisar tarayya a hankali wajen yin abin da ya dace a kan kudurin, ba a yi karfa-karfa domin a kawo dokar ba.
Malami ya yi lacca a kan kudirin haraji
Rahoto ya zo cewa Abubakar Abdussalam Babangwale ya ce kyau a zamantar da noma da kiwo domin ganin yadda ake kawo sauyi.
Malamin hadisan Manzon Allah SAW ya yi kira ga shugabanni su daina biyewa siyasa da ginin gadoji, su inganta rayuwar jama'a.
Idan aka dauki shawarwarin Abubakar Babangwale, ko an canza tsarin haraji, Arewa ba zata cutu ba domin kuwa ta rike harkokin noma.
Asali: Legit.ng