Gwamnonin Arewa 5 da na Kudu 5 da suka fi amfana da harajin VAT a Najeriya
- Alkaluma sun nuna Legas ce jihar da ta fi kowace cin moriyar harajin VAT
- Kano, Kaduna, Katsina suna cikin jihohin da suke tashi da kaso mafi tsoka
- Jihohin Nasarawa da Bayelsa sun samu 10% na abin da aka ba jihar Legas
Nigeria - Jihohin Arewacin Najeriya biyar da wasu biyar daga kudancin Najeriya sun karbi N373.84bn daga cikin N836.51bn da aka samu daga VAT.
Jaridar Punch tace wadannan jihohi goma sun karbi wadannan kudi ne a cikin watanni 14.
Binciken da hukumar tattara alkaluma na kasa watau NBS ta fitar a game da kason FAAC ya bayyana abin da aka ba jihohi tsakanin farkon 2020 da 2021.
Jihohin da ke gaba a cin VAT
Jihohin da ke kan gaba wajen samun kudi daga harajin VAT a wannan lokacin su ne:
1. Lagos (N153.94bn)
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Kano (N32.48bn)
3. Oyo (N29.85bn)
4. Rivers (N28.43bn)
5. Kaduna (N24.75bn)
6. Katsina (N22.72bn)
7. Delta (N20.91bn)
8. Bauchi (N20.49bn)
9. Anambra (N20.14bn)
10. Jigawa (N20.13bn).
Gwamnonin da ke yankin Kudu maso yamma sun samu N256.21bn, sai na Arewa maso yamma suka tashi da N154.41bn, na Kudu maso kudu sun ci N119.88bn.
Rahoton yace jihohin Arewa maso gabas sun samu N107.43bn, na Arewa maso tsakiya sun karbi N106.58bn. Abin da kudu maso gabas suka ci shi ne N91.99bn.
Su wanene jihohin da ba su samun kaso mai tsoka?
Jihohin da ba su samun wasu kaso mai tsoka daga abin da aka tattara a asusun VAT su ne:
1. Nasarawa (N15.36bn)
2. Bayelsa (N15.79bn)
3. Taraba (N16.23bn)
4. Gombe (N16.33bn)
5. Kwara (N16.35bn)
6. Ekiti (N16.46bn)
7. Yobe (N16.90bn)
8. Abia (N17.03bn)
9. Ebonyi (N17.04bn)
10. Cross River (N17.17bn).
Gwamnatin tarayya na raba abin da aka tara a asusun harajin VAT ta hanyar la’akari da adadin mutanen da ke jiha, abin da aka samu a jiha da kuma daidaito.
Ajuri Ngelale ya yi wa Wike kaca-kaca
A makon nan ne aka ji Ajuri Ngelale ya caccaki gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kan matsayarsa a game da batun VAT, yace ba a fifita jihohin Arewa.
Ajuri Ngelale wanda shi ne ke taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen hulda da jama’a ya soki kabilancin da gwamnan yake nuna wa a lamarin.
Asali: Legit.ng