Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban Miyetti Allah, Sun Sace 'Yarsa, Budurwa da Matarsa
- Yan bindiga sun hallaka shugaban rikon kwarya na Miyetti Allah a Katsina, Alhaji Amadu Surajo, tare da wasu mutum uku
- Yayin harin, an sace matan Surajo biyu da 'yarsa a harin da ya faru a kauyen Mai Rana da ke karamar hukumar Kusada
- Hukumomin tsaro sun fara bincike kan harin, yayin da aka binne mamatan bisa ka’idar Musulunci, wadanda suka ji rauni suna asibiti
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Katsina - Wasu 'yan bindiga sun kashe shugaban rikon kwarya na Miyetti Allah a Katsina, Alhaji Amadu Surajo a wani mummunan hari.
Lamarin ya auku ne a kauyen Mai Rana da ke karamar hukumar Kusada, daga ranar Asabar da dare zuwa safiyar Lahadi 5 ga watan Janairun 2025.
Yan bindiga sun hallaka shugaban Miyetti Allah
The Guardian ta ce yayin harin, an kashe wasu mutum uku, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Amadu Surajo ya zama shugaban rikon kwarya bayan bacewar shugaban MACBAN a Katsina, Munnir Lamido, a watan Yunin 2024.
Tun bayan bacewar Lamido, babu wani labari da aka samu game da shi, duk da cewa an gano motarsa da wayoyinsa a kusa da Maraban Jos, Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun yi garkuwa da matan Surajo guda biyu da 'yarsa, dalibar jami’a.
Sai dai, daga bisani wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa yan bindiga sun saki matar sa ta farko.
An birne marigayin da sauran mamata
Bayan wannan mummunan hari, hukumomin tsaro sun fara bincike kuma sun tura jami’ansu zuwa yankin domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali.
An birne gawar Surajo da sauran mamatan a safiyar yau Lahadi bisa ka'idar Musulunci, yayin da wadanda suka ji rauni ke karɓar magani.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, ASP Abubakar Aliyu, bai bayar da karin bayani ba a lokacin hada wannan rahoto.
Kotu ta amince a tsare shugaban Miyetti Allah
Mun ba ku labarin cewa shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo zai ci gaba da zama a hannun hukumomin tsaron kasar nan.
Wannan ya biyo bayan hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya, Mai Shari'a Emeka Nwite ya yanke kan bukatar DIA.
Hukumar leken asirin sojin kasa ta shigar da Bodejo kara bisa zargin ta'addanci da kai wa sojoji hari a Nasarawa.
Asali: Legit.ng