Malamin Addini Ya Fara Azumin Kwanaki 100, Ya Hango Masifar da Ke Tunkaro Duniya

Malamin Addini Ya Fara Azumin Kwanaki 100, Ya Hango Masifar da Ke Tunkaro Duniya

  • Fasto Enoch Adeboye ya ayyana fara azumin kwanaki 100 domin rokon ubangiji ya kare barkewar yaƙin duniya na Uku
  • Malamin addinin ya ce lallai akwai bukatar hana barkewar yakin, kuma ya yi kira ga jama'a da su dage da addu’o’i kan rikice-rikice
  • Adeboye ya yi hasashen nasarori a wannan shekara, ya na mai ba 'yan Najeriya shawarar abin yi domin fita daga matsin rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - Babban limamin Cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya ayyana azumin kwanaki 100 da addu'a domin neman zaman lafiya da hana barkewar yaƙin duniya na Uku.

Yayin taron Holy Ghost Service na farkon shekarar 2025 a Redemption City da ke jihar Ogun, Adeboye ya nuna damuwa kan rikice-rikicen da ke kara yawaita a duniya.

Kara karanta wannan

'Na san za a zage ni': Tinubu ya fadi shirin da yake yi wa Najeriya

Malamin addinin Kirista ya ayyana azumin kwanaki 100 ga mabiya cocin RCCG
Shugaban cocin RCCG, Fasto Adeboye ya ayyana azumin kwanaki 100 ga mabiyansa. Hoto: @rccghq
Asali: Twitter

Shugaban Cocin RCCG zai fara azumi

Malamin ya gargadi duniya cewa idan ba a shawo kan waɗannan matsaloli ba, za su iya rikidewa zuwa wani babban rikici mai girman gaske, inji rahoton PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya kamata mu yi addu’a domin hana sababbin yaƙe-yaƙe da tabbatar da cewa tsoffin rikice-rikice ba za su yi kamari ba."

- Fasto Adebayo.

Adeboye ya yi bayani kan yadda za a gudanar da azumin, inda ya ce waɗanda suka wuce shekara 70 ba za su cika azumin kamar kowa ba.

Fasto Adebayo ya tsara azumin kwana 100

Shugaban Cocin RCCG ya ce:

“Idan kana da shekara 70 zuwa sama, addu’o’inka kawai sun isa zuwa ga ubangiji, ba sai ka yi amfani da azumi wajen aika sakonka ba.”
“Amma idan ka dage kan cewa kana son yin azumin, za ka iya karya azumi da karfe uku na rana. Masu shekara 80 zuwa sama za su karya da karfe 12.”

Kara karanta wannan

Fitaccen Fasto a Najeriya ya yi aikin Hajji a Saudiyya? Adeboye ya fede gaskiya

Malamin ya ce azumin kwanaki 30 na farko zai shafi addu’o’i na neman ci gaban Najeriya, ciki har da yin addu’a kan cin hanci da matsin tattalin arziki.

Fasto Adebayo ya tsara addu'o'i ga mabiyansa

Adeboye ya kara da cewa wasu daga cikin addu’o’in za su kasance masu “zafi,” da nufin shawo kan masu lalata lamuran ƙasar nan.

Ya gargadi mabiya da su mai da hankali a lokacin azumin, yana cewa:

“Idan kana cikin azumi, ka rage magana. Ka tafi coci da karfe 6 na yamma don addu’a tare da mutane.”

Adeboye ya yi hasashen cewa wannan shekarar za ta kawo manyan ci gaba da nasarori ga mutane da dama.

Malami na so a yiwa duniya addu'a

A cewar malamin:

“Ubangiji ya ce ranar da mutane da yawa suke jira za ta zo wannan shekarar. Za a samu dumbin biki da auratayya."

A matakin duniya, ya yi kira ga addu’o’i domin hana yawaitar bala’o’i irin su ambaliyar ruwa, hadurran gobara da guguwar iska mai tsanani.

Kara karanta wannan

'Ku dage da addu'a;" Malamin addini ya hango abin da zai faru da Najeriya a 2025

Ya ja hankali da cewa:

“Ubangiji yana son mu yi addu’a don hana waɗannan bala’o’i da kuma sababbin yaƙe-yaƙe. Dole mu tabbatar da cewa tsoffin rikice-rikice ba za su yi kamari ba.”

Malami ya hango abin da zai faru a 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban Cocin Freedom Apostolic Revival, Fasto Samuel Adebayo Ojo, ya ce wahalhalun Najeriya za su kare nan da 2025.

A wani taron shekara-shekara a Ori Oke Ogo, Ibadan, ya bayyana cewa 2025 za ta zama shekara ta kwanciyar hankali da alheri.

Faston ya ce wannan shekarar za ta kawo farfadowa, waraka, da ci gaba, yana kira ga mutane su kasance da kyakkyawan fata da yakini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.