Fasto Ya Bada Babbar Gudummuwa a Wurin Buɗe Sabon Masallaci, Musulmi Sun Sha Mamaki

Fasto Ya Bada Babbar Gudummuwa a Wurin Buɗe Sabon Masallaci, Musulmi Sun Sha Mamaki

  • Domin kara danƙon zumunci da zaman lafiya, Fasto Yohanna Baru ya ba da gudummuwa ga sabon masallacin da aka gina a Tudun Biri
  • Malamin cocin ya ba masallacin sababbin butocin alwala, tabarmu da itatuwan da za a dasa a wurin taron buɗewa ranar Juma'a
  • An buɗe sabon masallacin ne tare da addu'o'i na musamman ga waɗanda harin bom ya rutsa da su a Tudun Biri shekara guda kenan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Babban limamin cocin bishara da rayuwa ta Kirista, Fasto (Dr.) Yohanna Buru, ya bayar da gudunmuwa ga sabon babban masallacin da aka gina a Tudun Biri.

An gina babban masallacin ne a kauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a Arewa maso Yamma.

Taswirar jihar Kaduna.
Fasto ya ba da gudummuwa a wurin bude sabon Masallaci a jihar Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Abubuwan da fasto ya ba sabon Masallaci

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Limamin da ake fargabar ya bace, ya bayyana kwatsam bayan kwanaki 25

Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa malamin cocin ya ba sabon masallacin gudummuwar itatuwan da za a dasa, tabarmi da kuma butocin alwala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faston ya yi haka ne domin ƙara dankon alaka tsakanin musulmi da kiristoci da haɗin kai tsakanin addinai mabanbanta a kauyen.

Fasto Yohanna Buru ya gabatar da gudummuwar ne a yayin taron bude masallacin wanda ya gudana a Tudun Biri jiya Juma’a.

An yi addu'o'i ga waɗanda harin bom ya shafa

Taron buɗe masallacin wani ɓangare ne na bikin cika shekara guda da kuskuren jafa bama-baman da sojoji suka yi kan masu taron Maulidin Annabi SAW.

An gudanar da addu'o'i na musamman ga wadanda suka rasa rayukansu, sannan an bude sabon masallacin a hukumance domin fara sallolin farinta a cikinsa.

Dailin fasto na ba masallaci gudummuwa

Da yake jawabi, Fasto Yohanna Buru ya ce cocinsa ta kawo ziyara ne domin ba Musulmi gudummuwa da kuma ƙara dankon zumunci da zaman lafiya tsakanin Kirista da Musulmi a yankin.

Kara karanta wannan

Bidiyon abin da mutane suka yi wa Bola Tinubu bayan gama sallah a masallacin Juma'a

Ya ce gudunmuwar cocin ba wai don samar da kayayyaki ga masallacin ba ne, har ma da taimakawa wajen karfafa dankon zumunci tsakanin mabiya addinan biyu.

Musulmi sun karɓi kayayyakin hannu biyu

Da yake godiya ga cocin, Malam Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya karbi tallafin, ya gode wa Fasto Dakta Yohanna Buru bisa wannan gudummuwa.

Mallam Ibrahim ya ce al’ummar yankin sun taru ne domin gudanar da addu’o’i na musamman ga wadanda harin bam ya rutsa da su tare da bude sabon masallacin.

"Yau shekara guda kenan da wannan ibtila'i ya afku a taron maulidin Annabi Muhammad S.A.W.
"Muna matukar godiya da ƴan uwanmu kiristoci da suka nuna zaman tare har suka kawo mana gudummuwa a wannan masallaci," in ji shi.

Gwamna ya kaddamar da ayyuka a Tudun Biri

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya tuna da mutanen Tudun Biri bayan cika shekara ɗaya da kusakuren jefa bama-bamai kan ƴan Maulidi.

Gwamnan ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka da duka haɗa da sabon asibiti, cibuyar koyar da sana'o'i da kuma rabawa mutane tallafi a kauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262