Fadan Fulani da Manoma Ya Barke a Jigawa, an Samu Asarar Rayuka
- Wani faɗan Fulani da manoma da ya ɓarke a ƙaramar hukumar Miga ta jihar Jigawa ya jawo asarar rayukan mutum tara
- Wasu mutum huɗu kuma sun jikkata bayan da faɗan ya ɓarke a safiyar ranar Juma'a, 3 ga watan Janairun 2025
- Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta hannun kakakinta, ta tabbatar da aukuwar lamarin mara daɗin ji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - An samu tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma a jihar Jigawa.
Faɗan makiyayan da manoman dai ya auku ne a ƙauyen Gululu, da ke a ƙaramar hukumar Miga da ke jihar Jigawa.
Yadda rikicin ya auku
Jaridar Tribune ta rahoto cewa Magajin Garin Gululu, Malam Muhammad Sarkin-Dori, ya ce lamarin ya auku ne a ranar Juma'a da safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa rikicin ya auku ne bayan wasu ɓarayi da ake zargin Makiyaya ne sun yi sata a wani shagon sayar da kayayyaki.
"Mun tashi mu kaga ɓarayi sun ɓalle wani shagon kayayyaki. Wasu mutane suka bi sahun ɓarayin, inda suka tsinci kansu a wata rugar Fulani. A nan ne aka yi ɗauki ba daɗin."
- Malam Muhammad Sarkin-Dori
Ƴan sanda sun yi ƙarin haske kan lamarin
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya bayyana cewa bayan mutanen garin sun bi sahun ɓarayin, sai Fulani suka riƙa harbinsu da kwari da baka inda suka raunata mutum huɗu.
Kakakin ƴan sandan ya ce daga sai mutanen ƙauyukan suka yi tururuwa, suna farmakar Fulani tare da ƙona gidajensu a ƙananan hukumomin Miga da Jahun.
"Bayan samun rahoton, tawagar ƴan sanda daga Miga da Jahun sun garzaya zuwa wajen, domin duba lamarin tare da dawo da doka da oda."
"Abin takaici, an gano gawar mutane tara. An kai gawarwakin zuwa asibitocin Miga da Jahun inda likita ya tabbatar da mutuwarsu."
DSP Lawan Shiisu Adam
Makiyaya da manoma sun fafata a Nasarawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya ya jawo asarar rayukan mutum uku a jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, ya bayyana cewa mummunan rikicin dai ya auku ne a ƙauyen Dogon Dutse da ke tsakanin ƙananan hukumomin Nasarawa da Toto.
Asali: Legit.ng