'Shan Giya da Sigari ba Zunubi ba ne': Malamin Addini Ya Jawo Magana a Hudubarsa
- Wani fitaccen Fasto a Najeriya, Abel Damina ya yi magana kan haramcin shan sigari ko giya a addinance
- Faston ya ce shan sigari da giya ba zunubi ba ne, yana mai jaddada cewa yana koyar da ceto ne, ba ɗabi'a ba
- Maganganunsa sun jawo muhawara, inda wasu ke yabonsa kan koyarwar ruhaniya, wasu kuma suna ganin yana rage muhimmancin ɗabi'u
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Uyo, Akwa Ibom - Babban malamin addinin Kirista, Fasto Abel Damina ya bayyana dalilin da yasa shan giya da sigari ba zunubi ba ne.
Faston ya ce shan sigari ko kuma giya ba zunubi ba ne illa kawai dabi'u ne marasa kyau ga dan Adam.
Fasto ya magantu kan shan giya da sigari
Hakan na kunshe ne a cikin wasikar bikin sabuwar shekara ta 2025 da muke ciki, wanda shafin @oxygist ya wallafa bidiyon a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto Damina ya bayyana wa mabiyansa cewa babu zunubi don ka ci ka sha inda ya jaddada cewa shan giya ba zunubi ba ne.
Sai dai ya ce shan sigari da giya zai iya lalata wa mutane jikinsu kamar yadda kowa ya sani amma ba zunubi ba ne.
“Ba za ka zama mai zunubi ba saboda cin abinci da sha, na fada muku a da, shan giya ba zunubi ba ne.”
“Ba don koyar da ku ɗabi'a kuka zo ba, amma don koyar da ku ceto ta ban-gaskiya cikin Almasihu."
“Ya kamata ku sani cewa idan kuna shan sigari, zai iya lalata jikin ku, idan kuka sha giya, kuna iya faɗuwa cikin rami, wannan abubuwan ya kamata ku koya tun daga gida."
- Abel Damina
Fasto ya fadi babban abin da yake koyarwa
Faston ya ƙara da cewa babban aikinsa shi ne koyar da ceto ta wurin ban-gaskiya cikin Almasihu, ba wai mayar da hankali kan ƙa'idojin ɗabi'a ba.
Maganganunsa sun jawo muhawara, inda wasu suke ganin yana rage muhimmancin ɗabi'a, yayin da wasu ke yabonsa.
Fasto ya shiga matsala kan suka Musulmi
Kun ji cewa wani Fasto a jihar Oyo ya ci zarafin wani Musulmi da matansa biyu saboda yanka rago kusa da cocinsa.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Iseyin da ke jihar inda Kungiyar CAN ta dauki mataki kan Faston.
Daga bisani Kungiyar a yankin ta ziyarci shugabannin Musulmai domin ba su hakuri kan abin takaicin da ya faru.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng