Ba haram bane shan giya indai kadan ce - inji wani malami
Wani malamin addini a kasar Misira mai suna Khalid Al Gendy yayi katobara inda ya bada fatwar cewa wai idan mutum yasa giya indai har bata sashi maye ba to bai aikata laifi ba.
Wannan fatawa ta sabawa mafi yawan mabiya addinin musulunci a kasar dama saura duniya baki daya.
Malamin Al Gendy ya bayar da wannan fatawar ne a cikin wani shirin gidan Talabijin na DMC inda ake yo tambaya kuma malamai su bayar da ansa dai dai da fahimtar su.
Malamin Al Gendy ya ce shi musulunci mayen da giya ke sawa ne ya hana amma ba wai ita kanta shan giyar ba.
Malamin ya ci gaba da bayyana wanda yayi maye a matsayin wanda bai iya gane damar sa daga hagu.
A wani labarin kuma, Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya watau Nigerian Prisons Service (NPS) Ja’faru Ahmed a jiya ya bayar da haske game da shirin da hukumar sa take yi wajen samun izinin daukar ma'aikata har 6,545 a matsayi daban-daban.
Shugaban Ja’faru Ahmed ya kuma ce shirin zai lakume zunzurutun kudi har N6biliyan don cimma nasarar hakan.
Kontolan ya kuma sanar da cewa hukumar tasa tana nan zata fito da wani shiri don bunkasa harkar noma irin na zamani a gidajen yarin fadin kasar nan domin yan gidan yarin su rika ci da kan su da kansu.
Asali: Legit.ng