Yadda Tinubu Ya Taimaka Wajen Fallasa 'Sirrin' Janar Abacha a wajen Bayahude
- Sanata Babafemi Ojudu ya bayyana yadda Bola Tinubu ya yi rikodin din wata tattaunawa da wani lauya kan sata da aka zargi Janar Sani Abacha da yi
- Rikodin din ya bayyana yadda Abacha ya karkatar da kimanin Dala biliyan 5 zuwa asusun bankuna a kasashen waje, ciki har da Amurka, Birtaniya, da Switzerland
- Duk da hadin kan Tinubu wajen tattara bayanan, ya yi kokarin hana wallafa labarin, amma Sanata Ojudu ya dage har aka buga shi a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sanata Babafemi Ojudu ya tono bayanai a wata hira da ya yi da Edmund Obilo kan sabon littafinsa mai suna Adventures of A Guerrilla Journalist.
Tsohon dan majalisar ya bayyana yadda shugaba Bola Tinubu ya yi rikodin din wata tattaunawa da wani Bayahuden lauya da ya fallasa cin hanci a lokacin Janar Sani Abacha.
The Cable ta wallafa cewa Ojudu ya ce rikodin din ya taimaka wajen fallasa cin hanci da rashawa da ake zargi an yi karkashin gwamnatin Abacha daga 1993 zuwa 1998.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Tinubu ya tattara sirrin Abacha
Sanata Ojudu ya ce yayin da yake gudun hijira a Birtaniya, Tinubu ya kai shi wajen wani lauya Bayahude da ya yi alkawarin bayyana yadda Abacha ya karkatar da dukiyar kasa.
Yayin da aka fara tattaunawa, Tinubu ya nemi zuwa bandaki, amma daga baya ya bayyana cewa ya sauya bangaren kaset din rikodin ne ba tare da sanin lauyan ba.
Business Day ta wallafa cewa Sanata Ojudu ya ce lauyan ya bayyana sunayen wadanda suka taimaka wa Abacha wajen satar kudin a cikin rikodin din Tinubu.
An wallafa labarin Abacha duk da barazana
Sanata Ojudu ya kara da cewa, bayan dawowa gida, Tinubu ya nemi hana shi wallafa labarin, amma ya dage ya buga shi, wanda ya girgiza gwamnatin Abacha.
“Tinubu ya ce: ‘Idan ka buga, za ka mutu.’
Na ce masa: ‘Na shirya wallafawa, kuma idan za su kashe ni, to, su kashe ni.’”
- Sanata Ojudu
Matsayar Ojudu kan takarar Tinubu
Duk da zaman tare da suka yi a baya, Ojudu ya ce ya ki goyon bayan Tinubu a zaben 2023, inda ya ce ba cin amana ba ne ya yi hakan ne bisa ga matsayar sa ta siyasa.
Ojudu ya ce Tinubu shugaba ne mai dabaru, amma ya sha bamban da ra’ayin da zai iya goyon baya.
Tinubu ya ki karbar ministan 'Yar'adua
A wani rahoton, kun ji cewa an bayyana yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ki yarda ya karbi matsayin minista a gwamnatin Yar'adua.
Sanata Ojudu ya ce shi ya gargadi Bola Tinubu da cewa ya nisanci karbar mukamin lura da matsayin da yake da shi a jam'iyyar adawa ta wancan lokacin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng