Yadda Tsohon Shugaban Amurka Ya Ceci Rayuwar Obasanjo har Ya Rayu Zuwa Yanzu

Yadda Tsohon Shugaban Amurka Ya Ceci Rayuwar Obasanjo har Ya Rayu Zuwa Yanzu

  • Olusegun Obasanjo ya ce marigayi Jimmy Carter yana daga cikin wadanda suka taimaka wajen kasancewarsa rayayye a yanzu
  • An ce tsohon shugaban Amurkar ya rasu a ranar 29 ga Disambar 2024 inda ya shiga sahun shugabannin da suka yi tasiri a duniya
  • A wata tattaunawa, Obasanjo, ya ce Najeriya ta yi rashin babban aboki tare da tuno irin gudunmawar da Carter ya ba kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abeokuta - Olusegun Obasanjo ya ce marigayi shugaban Amurka, Jimmy Carter, yana cikin wadanda suka taimaka ya rayu har zuwa yanzu.

Jimmy Carter ya rasu a ranar 29 ga Disambar shekarar da ta gabata, yana da shekaru 100 a lokacin rasuwarsa.

Olusegun Obasanjo ya tuno yadda suka yi rayuwa da marigayi tsohon shugaban Amurka
Obasanjo ya ba da labarin taimakon da tsohon shugaban Amurka ya baiwa rayuwarsa. Hoto: @historyinmemes, @Oolusegun_obj
Asali: Twitter

Tsohon shugaban Amurka ya ceci Olusegun Obasanjo

Obasanjo, wanda ya kasance shugaban mulkin soja a 1978 lokacin da Jimmy Carter ya ziyarci Najeriya, ya yi magana da Channels Television a gidansa na Abeokuta.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban ya bayyana cewa Carter ya ba da gudummawa wajen dorewar rayuwarsa har zuwa yau, yana tuna abotar da suka kulla tare da Carter.

Amma bai yi karin bayani kan yadda Carter ya ceci rayuwarsa ba. Ya dai ce Najeriya da nahiyar Afirka sun rasa aboki yayin da duniya ta rasa mai kare adalci.

Alakar lokacin mulkin Obasanjo da Carter

A cewarsa, marigayi Carter ya ba da gudummawa mai girma wajen inganta dangantakar Najeriya da Amurka a lokacin da yake shugaban Amurka.

Obasanjo ya kasance shugaban mulkin soji daga watan Fabrairu na 1976 zuwa Oktoba 1979, sannan kuma ya zama shugaban kasa na dimokuradiyya daga Mayun 1999 zuwa Mayun 2007.

Carter ya zama shugaban Amurka na 39 daga 1977 zuwa 1981. Bayan barin fadar White House, ya yi aikin kare dimokuradiyya da yakar cututtuka masu hadari.

Rayuwar Carter ta zama abar koyi ga Amurkawa

An haifi Carter a kauyen Plains na jihar Georgia, ya rasu a gidan da ya siya tare da matarsa wadda suka yi aure na tsawon shekaru 77.

Kara karanta wannan

Daga zuwa sasanta rikicin miji da mata, an kashe wani malamin addini a Najeriya

Rayuwar Carter ta kasance mai sauki kuma ta zama abin koyi ga 'yan Amurka da dama, duk da cewa sauran shugabannin Amurka ba su dauki salon irin rayuwarsa ba.

Misali, zargin keta dokar aure na John F. Kennedy, al'amuran soyayya na Bill Clinton da ma'aikatan White House, da kuma manyan hare-haren shahararrun shugabannin Amurka.

Mutuwar Carter: Obasanjo ya aika sako ga shugabanni

A wani labarin, mun ruwaito cewa Olusegun Obasanjo, ya ba shugabannin Najeriya shawara kan shugabanci nagari tare da yin koyi da marigayi Jimmy Carter.

Cif Obasanjo ya bayyana marigayi Carter a matsayin jagora wanda ya nuna kaskantar da kai da dawainiya lokacin mulkinsa, wanda hakan ya kawo ci gaba a Amurka.

Obasanjo ya jinjina wa Carter bisa kokarinsa wajen kawo zaman lafiya, musamman tsakanin Isra’ila da Masar da shiga tsakanin rikicin Falasdinawa da Isra’ilawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.